Babbar kotun gwamnatin tarayya dake Abuja ta ce ba za a bai wa Hamisu Bala da aka fi sani da Wadume ba, tare da mutum shida wadanda ake zarginsu da aikata garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka.
Kotun ta hana bada belin ne bayan da lauyan masu kare wadanda ake zargi ya nemi bukatar hakan.
Mai Shari’a Binta Nyako ne ta bayyana hakan a ranar Laraba, inda ta nemi da cewa a yi maza a fara gabatar da shari’ar, inda ta umurci da a mayar da wadanda ake zargi zuwa kurkukun Kuje daga inda ake tsare da su a SARS a halin yanzu ta yadda lauyoyinsu za su samu damar ziyartarsu cikin sauki.
Mai Shari’a Nyako har wala yau ta bada umurnin a bai wa wadanda ake kara damar ganawa da likitoci domi duba lafiyarsu.
A ranar 6 ga watan Agustan 2019, jami’an tsaron ‘yan sandan Nijeriya na ofishin Sufeto janar na ‘yan sandan Nijeriya, IRT-IGP, suka cafke Wadume a garin Ibi ta jihar Taraba bisa zarginsa da garkuwa da jama’a.