Kotu ta hana tsohon Rijistaran Jamb beli
A ranar Talata ne babban Kotu dake Abuja ta haramtawa tsohon Rijistaran Jamb Farfesa Dibu Ojerinde beli, kan tuhumarsa da hukumar ICPC da tayi da cin hanci.
Mai Shari’a Obiora Egwuatu shine ya hana belin lokacin da mai Shari’a wanda ke kareshi P.O Olorunishola, ya rokeshi da bukatar hakan.
KARANTA:-Ndume ya bada Miliyan 40 tallafi ga Manoma, Yan kasuwa da Ɗalibai
Hakan ya biyo bayan da mai Shari’a dake Kare hukumar ICPC Ebenezer Shegunle ya musanta hakan.
Ojerinde, an makashi kotun ne kan tuhumarsa da akeyi kan rashin cikakken bayani da yayi, wajan kashe kudade kimani miliyan dari tara.