Daga: Abbas Yakubu Yaura
Wata babbar kotun birnin tarayya Abuja a ranar Juma’a ta hana ‘yan jarida daukar labarai da kuma shaidar yaran marigayiya mawakiyar bishara Osinachi.
A cewar kotun, hakan ya biyo bayan amincewa da bukatu uku na baki da lauyan mai shigar da kara Aderonke Imana ya gabatar a ranar 22 ga watan Yuni.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/ka-dawo-da-najeriya-yadda-ka-same-ta-kafin-ka-tafi-daura-sakon-wani-dan-fafutuka-ga-buhari/
Lauyan ya shigar da karar ne a yayin zaman kotun a kan zargin kisan kai da ake yi wa Peter Nwachukwu, mijin marigayiyar wanda a halin yanzu yake tsare a gidan yari.
Osinachi, mai suna Ekwueme crooner da ta mutu a ranar 8 ga watan Afrilu sakamakon rikicin cikin gida, an binne ta a ranar 25 ga watan Yuni a mahaifarta Isochi Umunneochi a jihar Abia.
A wani labarin kuma Wani Alhaji daga Gombe kuma Malami a Jami’ar Jahar Dr Abdulrahman Mai Gona ya rasu a ranar Alhamis a Ƙasar Saudi Arabia.
Da yake sanar da mutuwar Alhajin a cikin wata sanarwa daga Shugaban Hukumar Kyautata Jindaɗin Alhazai ta Jahar Gombe, daga Shugabar Kula da Kafafen Yaɗa Labaru Hauwa Muhammad, yace Alhajin ya rasu bayan gajeruwar rashin lafiya.
Mai Gona, Malami a Sashen koyar da ilmin Addinin Musulunci, yana daya daga cikin mamban Hukumar Gudanarwa na Gwamna Muhammadu Yahaya domin kaisu ƙasa mai tsarki.
Ya bayyana cewa Marigayin ya rasu bayan rashin lafiya, kuma za’a binne shi kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada.
“Mutuwar Alhaji Dr Abdulrahman Umar Mai Gona ya faru ne a yau (Alhamis) a Saudiyya bayan gajeruwar rashin lafiya. Gona yana ɗaya daga cikin sababbin wanda aka naɗa a Hukumar Gudanarwa na Hukumar Kula da Kyautata Jindaɗin Alhazai ta Jahar Gombe, da Gwamnan Jahar Gombe Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya.
“ya kasance malami a sashen kula da ilmin Addinin Musulunci, Jami’ar Jahar Gombe. Hukumar na bakin ƙoƙari domin tabbatar da an rufe shi kamar yadda musulunci ya tanada. Allah ya jikansa sa, ameen,” Inji Sanarwa.
Shugaban Hukumar Kyautata Jindaɗin Alhazai na Ɓangaren Lafiya Dr. Usman Shuaibu Galadima wanda aya tabbatar da faruwar lamarin yace Mai Gona an kawo da misalin ƙarfe 1 inda yayi saurin bashi kulawa.
A cewar sa, lamarin yayi ƙamari, dandanan rashin lafiyar tayi nisa,daganan ya rasu.
Galadima yace ya ziyarci Asibitin kuma an bashi magani akan wata cutar daban.
Wani shaidar gani da ido yace Malamin Musuluncin saida ya furta kalmar Laila-illa-Allahu kafin ya rasu.
An kai gawar sa a Masallacin Harami domin yi mashi Jana’iza.
Mai Gona shine Alhaji na uku da ya rasu daga cikin Alhazan Najeriya.