Kotu ta Kori Ɗan Takarar Gwamnan PDP a Delta
Babban Kotun Tarayya dake Abuja ta kori Sherif Oborevwori a matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Jahar Delta a Jam’iyyar PDP domin Babban Zaɓen Shekarar 2023.
Mai Shari’a Taiwo Taiwo a ranar Alhamis ya gano cewa Oborevwori ya kai bayanan ƙarya ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta INEC, inda yayi ƙari akan takardun sa, domin Takarar Gwamna.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sai da na Gargadi Aregbesola kan harin da za’a kawo wa Gidan Yarin Kuje — Sadiq
Jojin ya kuma umarci INEC da PDP data sanya David Edevbie a matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Jahar Delta a PDP a Babban Zaɓen Shekarar 2023 a Jahar.
Oborevwori wanda shine Shugaban Majalisar Dokoki ta Jahar Delta, ya zama Ɗan Takarar PDP bayan zaɓen fidda Gwani da aka yi a ranar 25 ga watan Mayu na Shekarar nan.
A wata ƙara da Edevbie ya shigar, wanda ya kasance tsohon Kwamishinan Kuɗi a ƙarƙashin Gwamna James Ibori, Wanda ya zo na biyu, ya zargi Oborevwori da bayanan ƙarya a takardun sa da ƙare-ƙare a shekarun sa.