Kotun sauraron korafin zabe da ke zaman ta a Akure, babban birnin jihar Ondo, ta soke zaben Ikebgboju Gboluga, mamba a majalisar wakilai daga mazabar Okitipupa/Irele da aka zaba a karkashin inuwar jam’iyyar PDP.
Kotun ta soke zaben Gboluga ne a ranar Laraba bisa dalilin cewa bashi da hurumin yin takara a zaben ranar 23 ga watan Fabrairu, 2019, saboda mallakar takardun zama dan asalin kasar Ingila tare da yin rantsuwar zama mai biyayya ga kasar kafin a bashi takardun shaidar zama dan kasar.
Kazalika, kotun ta bayyana sunan Albert Akintoye na jam’iyyar APC a matsayin halastaccen wanda ya lashe zaben tare da bawa hukumar zabe ta kasa mai zaman kan ta (INEC) umarnin ta karbe shaidar cin zabe daga hannun Gboluga ta bawa Akintoye.