wata kotu dake zamanta a garin Ibandan ta raba aure sakamakon rashin kulawa.
Mai shari’a Ademola Odunade, ya Raba Auren Basirat olabode, da Mijinta Dauda, ne domin Kotu, ta Gamsu cewa a Halin yanzu babu Soyayya, a Tsakanin su, bayan suna da yara uku Wanda shekarun su daga 3 zuwa 11.
Kazalika Kotun ta yi umarni ga Dauda, cewa duk wata zai bada dubu sha biyar a matsayin kudin ciyarwa, sannan da biyan kudin makarantar ‘ya’yan sa, da kuma Rashin Lafiyar su.
A nata bangaren Kuwa, Basirat, wace ke zaune a ofofo, da ke Ibadan tace dama surukar ta ta tsane ta ba tun yau ba, inda tace ba wani abun alheri da ya taba hada su ko yaranta sai dai kullum burinta Danta ya sake ni tsawon shekaru 12 nan da muka yi, inji ta.
Na rasa daya daga cikin yarana wanda a nan ne na kara gane irin kin da take min.
Na rabu da shi tun watan janairu daga wancan lokacin da muka rabu baya bamu ci da sha nida yarana, inji Basirat.