Kotu ta sake bayar da umarnin kamo shugaban hukumar EFCC tare da garkame shi a gidan gyaran hali na Kuje.
Kotun tuni ta baiwa babban sifeton yan sanda umarnin kamo shugaban EFCC din, tare da tsare shi tsawon kwanaki 14.
KU KARANTA: Hukumar Shirya Gasar Premier Ta Zargi Man City Da Wasu Laifuffuka
A hukuncin da mai Shari’a a babbar kotun jihar Kogi Justice R.O Ayoola ya yanke, ya amince da bukatar da aka nema wajen tsare shugaban na EFCC saboda kin bin umarnin kotu.
A watan Nuwamba 2022 ne kotun ta bayar da umarnin ga EFCC kan aiwatar da bukatun kotun kan wani mutum Ali Bello wanda ya shigar da kara gaban ta.
Ali Bello ya shigar da karar ne kan kama shi da EFCC tayi, tare da tsare shi ba bisa ka’ida ba, inda kuma kotu ta amince da karar sa.
Hakan ya sanya kotun ta yi watsi da bukatar hukumar EFCC din, na neman jingine wancan hukunci bisa hujjar cewa ba shi da inganci.
A wani labarin kuma: EFCC Ta Kama Wani Manajan Banki Kan Boye Sabbin Kudin Naira
Jami’an Hukumar EFCC sun kama wani manajan ayyuka na wani babban bankin kasuwanci da ke yankin tsakiyar Abuja a ranar Litinin, bisa laifin kin sanya kudi a na’urar ATM.
DIMOKURAƊIYYA ta rawaito cewa wannan na zuwa ne duk da cewa Manajan yana rike da Naira miliyan 29 na sabbin takardun kudi na Naira a cikin bankin.