Wata babbar kotu a kasar Jordan ta samu dan uwan Sarkin kasar da kuma wani alkalin kotu da hannu dumu-dumu wajen kokarin hambarar da gwamnatinsa.
Duk da cewa mutanen biyu masu suna Bassem Awadallah da kuma Sharif Hassan dun musanta zargin da ake musu, amma hakan bai taka wa kotun burki na garkame su shekara 15 gidan yari ba.
An tsare mutanen biyu ne a watan Afirelu, bayan da tsohon Yariman Jordan mai jiran gado Prince Hamza ya faɗa komar hukumomi bisa zargin sa da hargitsa kasar.
To sai dai babu wani hukunci da aka yanke wa shi Prince Hamza a matsayin shi na dan uwa ga Sarkin kasar.