Mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya dake Abuja ya sanya ranar 1 ga watan Disamba, 2022 domin yanke hukunci kan tikitin takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Ogun a zaben shekarar 2023.
Mai shari’a Ekwo ya tsayar da ranar ne bayan ya yi muhawara da jam’iyyun.
KARANTA WANNAN LABARIN: Alkalai 9 Sun Samu Sauyin Wajen Aiki A Jihar Kano
A tsakiyar rikicin dai akwai Jimi Lawal da Oladipupo Adebutu, dukkansu ‘yan takarar gwamna a jam’iyyar PDP wadanda suka yi ikrari da kin amincewa da tikitin takarar.
Lawal wanda ya tsaya takarar gwamna a jam’iyyar PDP a ranar 25 ga watan Mayu, ya kalubalanci fitowar Adebutu, inda ya yi zargin cewa jam’iyyar ta yi amfani da jerin sunayen wakilai ba bisa ka’ida ba wajen gudanar da zaben.
Daga cikin sauran, Lawal ya yi rokon cewa a soke zaben fidda gwani na ranar 25 ga watan Mayu, sannan a gudanar da wani tare da ingantattun wakilan jam’iyyar.
Sai dai mai shari’a Taiwo Taiwo na babbar kotun tarayya a hukuncin da ya yanke a ranar 29 ga watan Yuli ya ki sauraron karar Lawal bisa hujjar cewa zaben fidda gwani na cikin gida ne na kowace jam’iyyar siyasa, ya kuma yi watsi da karar.
Daga bisani kotun koli a ranar 21 ga watan Nuwamba ta umarci babbar kotun tarayya da ta saurari karar da Lawal ya shigar a kan PDP da Adebutu.
Mai shari’a Ibrahim Saulawa na kotun kolin ya bayar da umarnin a gaggauta sauraron karar bayan da ya ce babbar kotun tarayya na da hurumin sauraren karar.
A zaman da aka yi na ranar, Mai shari’a Ekwo, bisa bin umarnin kotun koli, ya saurari karar cikin gaggawa ganin yadda shari’ar za ta tashi zuwa ranar 2 ga watan Disamba.
Mai shari’a Ekwo ya ce zai yanke hukunci a karar a ranar 1 ga watan Disamba, 2022.
A wani labarin kuma, Yanzu Yanzu: Kotu Ta Soke Takarar Wani Dan Takarar Gwamnan APC
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Fatakwal, a ranar Alhamis, ta kori dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Ribas, Tonye Cole.
Kotun ta soke takarar sa ne kan mallakar shaida zama dan kasa biyu, wato bayan Nigeria ya kuma samu shaidar zama ɗan wata kasar, inda aka ce Tonye Cole ɗan ƙasar Burtaniya ne.
Kotun ta kuma ce APC ba ta bi dokar zabe da ta kawo Cole a matsayin dan takarar jam’iyyar ba.