tambuwal

Kotu Ta Tabbatar Da Tambuwal A Matsayin Gwamnan Sakkwato

Kotun sauraron kararrakin zabe wadda ta yi zama a Abuja ta yi watsi da karar da Ahmad Aliyu na APC ya shigar a gabanta, inda ya kalubalanci nasarar da Gwamna Aminu Tambuwal na PDP ya samu a jihar Sakkwato a zaben Gwamnan 2019.

Kotun ta ce jam’iyyar APC da dan takararta sun kasa gabatar da kwararan hujjoji da za su nuna an saba wa ka’idojin zabe da kuma dokar zabe ta 2010.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *