A ranar Asabar da ta gabata ne kotun sauraren korafin zaben gwamnan jihar Nasarawa inda dan takarar PDP ya shigar ya na kalubalantar yadda hukumar zabe ta bayyana dan takarar APC, Injiniya Abdullahi Sule, matsayin wanda ya yi nasara.
Kotu ta kori koken zaben gwamnan jihar Nasarawa da jam’iyyar PDP da dan takarar ta, David Emmanuel Ombugadu, suka mika a kan jam’iyyar APC, da hukumar zabe mai zaman kanta, INEC da Gwamnan jihar Abdullahi Sule.
Alkalin da ya yanke hukuncin cikin sa’o’i 9, Mai shari’a Abba Bello Mohammed, ya ce, masu karar sun gaza gamsar da kotun bisa ga ingantatun hujjoji, don haka ne aka yi watsi da ita.
Kamar yadda ya ce, mai kara ya kamata ya tabbatar da zarginsa da ingantattun shaidu na cewa an yi dangwale, ta da hargitsi yayin zabe da sakamakon karya da sauransu.
Ya ce, karar ba ta bi tanadin dokokin zabe na 2010 ba, don haka ne aka kasa gaskata ikirarin. Alkalin ya kara da cewa, babu daya daga cikin shaidun da mai kara ya gabatar da ya iya bayyana ko takarda guda daya da za ta tabbatar da zargin.
Mataimakin gwamnan jihar, Emmanuel Akabe, da ya yi magana da yawun gwamnan a kan hukuncin ya ce, hukuncin ya tabbatar da cewa kuri’un mutane sun yi aiki.
Gwamnan jihar ya ce, wannan hukuncin na nuna cewa kuri’un mutane jihar sun yi amfani.
A yayin mai da martani ga hukuncin, lauyan mai kara, Affiku Gambo, ya ce za su kara bincike mai zurfi kafin su yanke hukuncin abin da za su yi nan gaba.