Kotun sauraren kara dake Sakkwato a ranar Litinin ta tabbatar da zaben Sanata Aliyu Wamakko a matsayin Sanata mai wakiltar Sakkwato ta Tsakiya. Inda kuma ta yi watsi da daukaka karar da Sanata Ahmad Maccido ya shigar gaban kotun yana kalubalantar hukuncin kotun sauraren kararrakin zaben majalisu.
A ranar 6 ga watan Satumba ne, kotun sauraren kararrakin zaben majalisu ta yi watsi da karar da Sanata Maccido na PDP ya shigar gabanta yana kalubalantar zaben Sanata Wamakko na APC.
Bisa rashin gamsuwa da hukuncin da kotun sauraren kararrakin zaben ta yanke, Sanata Maccido na PDP ya nufi kotun sauraren daukaka kara.
A hukuncin da ya yanke, Justice Ibrahim Saulawa wanda hukuncin Justice Hamma Akawu ya karanta, ya ce kotun sauraren daukaka karar ta tabbatar da hukuncin kotun sauraren kararrakin zabe.