Babbar kotun jihar Kano da ke zamanta a karamar hukumar Rano ta yi fatali da karin masarautun yanka hudu da gwamnatin jihar Kano ta samar a makon da ya gabata.
A zaman kotun na yau lauyan masu kara AB Mahmoud ya koka akan yadda gwamnatin jiha ta yi kunnen uwar shegu ga umarnin da kotun ta bayar na dakatar da tabbatar da sarakunan a ranar 10 ga wata.
A lokacin da ya ke yanke hukunci alkalin kotun mai shari’a Nasiru Saminu, ya rushe masarautu hudun da aka samar, tare da kuma ayyana masarautar Kano a matsayin halastacciyar masarauta daya tilo da ake da ita a Kano.
An dai dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 20 ga watan Yunin da za’a shiga.