Babbar Kotun Majistare dake zamanta a Fatakwal, ta Jahar Rivers ta tura wani ɗan shekara 22 Joshua Efe a gidan yari na Fatakwal, sakamakon zargin sa da lalata da yara guda huɗu a Babban Birnin Jahar.
Cikin yaran akwai ɗan shekara 9 , da 11, da 12 da shekaru 16.
Efe wanda yake zaune a Fatakwal, an yi ƙarar shi a dalilin yin lalata da yaran, da kuma lalata masu duburar su.

KARANTA WANNAN LABARIN: Da ɗuminsa: IG na Ƴan sanda ya isa wurin ginin daya rufta a Lagos
An kuma yi karar shi bayan ya lalata yaran, ta hanyar basu kyauta domin yayi lalatar, wanda hakan ya saɓawa sashe na 353 na Manyan masu laifuka na Jahar Rivers ta shekarar 1999.
Wanda ake ƙarar yace bai aikata laifin da ake zargin shi da aikatawa ba a lokacin da aka karanta mashi laifin, inda Babban Majistare Rita Oguguo ya tura shi a cibiyar gyaran aƙida har sai ranar 18 ga watan Nuwamba na shekarar 2021, domin duba yiwuwar bada shi beli da kuma sauraro.
Mai shigar da ƙarar Jane Okpamen daga ɓangaren masu kare haƙƙin bil’adama wanda yayi jawabi ga Manema labaru, ya bayyana fatan cewa za’ayi adalci akan lamarin, domin ya zamanto darasi ga wasu.
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta ruwaito cewar, wanda ake ƙarar bashi da lauya mai kare shi.
Comments 1