By Abbas Yakubu Yaura
Wata Kotun Majistare dake zaman ta a Makurdi ranar Juma’a ta ba da umarnin a tsare wani likita, Edwin Iordye, a gidan gyaran hali bisa zargin lalata da wata yarinya ‘yar shekara 15.
‘Yan sanda sun tuhumi Iordye, wanda ke zaune a Makurdi, da laifin yin fyade.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hukumar DSS ta cafke mutune 3 da daifin Bude cibiyar rajistar masu zabe ta jabu, da karbar kudade
Duk da haka, Alkalin Kotun, Mista Vincent Kor, bai dauki karar Iordye ba saboda rashin hurimin kotun.
Kor ya dage ci gaba da shari’ar har zuwa ranar 2 ga watan Agusta domin ci gaba da sauraren shari’ar.
Tun da farko, Lauyan masu shigar da kara, Insp Godwin Ato, ya shaida wa kotun cewa an karbi karar ne a CID na jihar, Makurdi, daga hedikwatar ‘yan sanda, sashe na D Makurdi, a ranar 16 ga watan Yuni.
Ato ya ce wata ‘yar uwar wanda abin ya shafa mai suna Blessing Tyokpe ta kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda na ‘D’ a ranar 13 ga watan Yuni.
Mai gabatar da kara ya ce yar uwar wanda abin ya shafa ta ba da rahoton cewa yar uwarta na fama da ciwon kafa kuma an kai ta wurin Iordye don yi mata magani.
Ya ce wanda ake zargin ya bukaci wanda abin ya shafa da ta cire mata kayanta domin ya shafa mata magani.
‘Yan sanda sun ce Iordye anan ya samu damar yi mata fyade.
Laifin, in ji shi, ya saba wa tanadin sashe na 284 na dokokin manyan laifuka na jihar Benue shekarar 2004.
(NAN)