By Abbas Yakubu Yaura
Wata Kotun Majistare dake Jihar Ekiti, reshen Ado Ekiti, ta bayar da umarnin tsare wani mai gadi mai shekaru 37 mai suna Olukayode Adebayo, har zuwa lokacin da za a ba da shawarar shari’a kan zargin yi wa karamar yarinya fyade a ranar Kirsimeti.
Wanda ake tuhumar yana gaban shari’a kan laifin fyade.
Laifin tuhumar ya bayyana cewa Adebayo “ana kyautata zaton ya aikata laifin fyade ga wata yarinya ‘yar shekara 13 a Peace Avenue, dake kan titin Afao, Ado Ekiti, ranar 25 ga watan Disambar shekarar 2021.”
A bayanin da ta yi wa ‘yan sanda, wadda abin ya shafa ta ce, “A ranar Kirsimeti, na je shagonmu ne bisa umarnin mahaifiyata na kawo mata ayaba da kum Goro. A kan hanya ta zuwa gida, wanda ake zargin yana kan babur, ya same ni a hanya, ya ce in hau babur don ya kai ni gida batare da nuna wani shakku ba sai yarda.
“A kan hanyarmu ta zuwa gida, ya kai ni wani gini da ba a kammala ba, ya kuma yimin fyade yayi tafiyar sa. Kuka na ne ya ja hankalin masu wucewa, suka kai ni gida. Na bayyana wa mahaifiyata lamarin kuma daga baya muka kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda.”
Dan sanda mai shigar da kara, Sufeto Sadiq Adeniyi, ya ce laifin ya sabawa sashe na 31 na dokar kare hakkin yara na jihar Ekiti na shekarar 2012.
Mai gabatar da kara, a cikin takardar da ya shigar, ya bukaci kotun da ta ci gaba da tsare wanda ake kara a gidan gyaran hali na Najeriya, dake Ado Ekiti, har sai an kammala binciken ‘yan sanda da kuma shawarwarin shari’a daga ofishin daraktan kararrakin jama’a.
Alkalin kotun, Mojisola Salau, ta amince da bukatar sannan ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare Adebayo, inda ta ce, “Tsarin wanda ake kara zai baiwa ‘yan sanda damar kammala bincikensu, yayin da mai gabatar da kara zai kwafi karar sannan ya aika ta zuwa ga ofishin DPP domin samun shawarar lauyan.”