Wata babbar kotun majistare da ke Ado Ekiti ta bayar da umarnin tsare wani matashi mai suna Kehinde Akeem dan shekara 34 bisa zargin yi wa wata yarinya ‘yar shekara 13 fyade a Ado Ekiti. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito
A cewar tuhumar, Kehinde Akeem, a ranar 20/08/2022 a Ado Ekiti ana zarginsa da aikata laifin fyade, wanda hakan ya sabawa sashe na 31 (2) na dokar kare hakkin yara na jihar Ekiti, 2012.
Da yake gabatar da karar da ya shigar gaban kotu, dan sanda mai shigar da kara, Insifekta Sadiq Adeniyi ya roki kotun da ta amince da bukatar a ci gaba da tsare wanda ake kara a gidan yari da ke Ado Ekiti domin baiwa ‘yan sanda damar kammala bincike tare da mika kundun bayanan shi na biyu zuwa gaban kotun.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zaben 2023: Ba Mu Rena Karsashin PDP, Da APC Ba, Amma Jam’iyar NNPP Zata Bada Mamaki—–Kwankwaso
A bayanin da ta yi wa ‘yan sandan, wadda aka yi wa Fyaden ta ce, “Ya zo siyan kunu ne a shagonmu, ya ce, ya manta kudi a gida, sai ya roki mahaifiyata ta bani dama in bi shi in karbi kudin, mahaifiyata ta ki amincewa amma bayan haka. wani lokaci mahaifiyata ta yarda, lokacin da muka isa gidansa ya ba ni mabudin bude kofa, na aje mai kunun, ina shiga dakinsa ya rike ni daga baya, ya kulle kofa ya tura ni kan gadonsa, nai ta yin kururuwa amma ya yi min fyade kafin makwabta su kawo min dauki, an yi masa mugun duka, da mahaifiyata ta zo, aka kai kararsa aka mika shi ga jami’an rundunar ‘yan sanda.
A hukuncin da ya yanke, Alkalin Kotun Mai shari’a Dolamu Kay-Williams ya bayar da umarnin a tsare wanda ake zargin a gidan gyaran hali na Najeriya da ke Ado Ekiti har zuwa lokacin da Daraktan shigar da kara na kasa ya bayar da shawara kan shari’a.
Daga bisani ya dage sauraron karar zuwa ranar 29 ga Satumba 2022 don ambato.
Yan takarar APC Kawai Zan Tallata A Zabe Mai Zuwa— Shugaba Buhari