Rundunar ‘yan sandan jihar Binue a ranar Litinin ta gurfanar da wani Kakule Aondonyega (18) a gaban wata kotun yankin Makurdi bisa laifin yin garkuwa da wata karamar yarinya da kuma yimata fyade.
Mai gabatar da kara, Insfecta Rachael Mchiave, ya shaidawa kotun cewa an shigar da karar ne a sashen binciken manyan laifuka (CID), dake Makurdi, ta wata rubutacciyar koke ta wata Dorcas Wajir.
Insfecta Mchiave ya ce mai shigar da kara ya yi zargin cewa a ranar 3 ga Mayu, Kakule Aondonyega na yankin Agina, a garin Zaki-Biam, dake karamar hukumar Ukum , ya yi garkuwa da ‘yar wansa, Dooshima Wajir, karamar yarinya, daga garin Tiontyu, karamar hukumar Tarka, inda take zaune tare da ‘yar uwarta, Jennifer. Wajir, ya kai ta wurinsa a Zaki-Biam ya yi lalata da ita.
Mai gabatar da kara ya ce yayin binciken ‘yan sanda, Aondonyega ya amsa laifinsa.
Alkalin kotun, Mrs Dooshima Ikpambese, ta bada umarnin tasa keyar wanda ake tuhumar zuwa a gidan yari na tarayya dake Makurdi, sannan ta sanya ranar 30 ga watan Yuni domin ci gaba da ambatonsa. (NAN).
A wani labarin Kuma na daban.
Yan tawayen Ambazonia Basu Farmaki Yan Najeriya ba—— Rundunar Soji Ta Kasa
Rundunar sojin Najeriya ta ce rahotannin da aka samu game da hare-haren da ‘yan awaren Kamaru (Ambazonian) sun kai wa wasu kauyuka hari, karya ne tsagwaranta
Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya.-Janar. Onyema Nwachukwu ne ya fitar da sanarwa a ranar Litinin.
Nwachukwu ya ce sojojin Najeriya da ke garin Danare sun samu bayanai tare da tattarawa al’ummar Bashu, wadanda ake zargin an kai musu hari.
Kakakin ya kara da cewa da isar su sun gano cewa babu wani kutse ko hari da aka yi a Bashu.
“A maimakon haka, ‘yan awaren sun kai hari Obonyi 2 da Njasha, wadanda dukkansu al’ummomi ne a Jamhuriyar Kamaru,” in ji shi.
Mutane hudu da lamarin ya rutsa da su, wadanda Yan Najeriya ne, sojoji da jami’an Hukumar Shige da Fice ta Kasa (NIS) sun ceto su.
Nwachukwu ya bada tabbacin baiwa sojoji kariya sannan ya shawarci jama’a da su kwantar da hankalinsu