Wata kotun majistare dake Ile-Ife ta tsare wani matashi dan shekara 24 mai suna Oluwatobi Falope a ranar Alhamis bisa zargin satar mayafin ruhuwa.
Dan sanda mai gabatar da kara, ASP Abdullahi Emmanuel, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne a ranar 14 ga watan Disamba, 2021, da misalin karfe 07:00 na dare, a makarantar Firamare ta Salvation Army, Oke-Atan dake Ile-Ife.
Emmanuel yace wanda ake tuhumar ya saci wasu abin ruhuwa da kudinsu ya kai Naira 25,000, na daga cikin kadarorin makarantar Salvation Army dake Ile-Ife.
Sai dai kuma Falope ya musanta zargina laifin aikata satar.
Mai gabatar da karar yace laifin ya ci karo da sashe na 390(9) na kundin laifuffuka, dokokin jihar Osun na shekarar 2002.
Lauyan wanda ake kara Mista J.O. Amole, ya nemi a bayar da belinsa a mafi sassaucin ra’ayi kuma ya yi alkawarin cewa wanda yake karewa ba zai yi tsallake beli ba, amma zai ba da wasu tabbatattu masu tsaya masa.
Alkalin kotun mai shari’a O.B. Adediwura ya shigar da wanda ake tuhumar belinsa kan kudi Naira 50,000, tare da tsayayyen wanda zai tsaya masa.
Adediwura ya bada umarnin cewa wanda zai tsaya masa dole ne ya rantse da wata takardar shaida, ya zauna a cikin ikon umarnin kotun kuma a tantance adireshin wajen da yake zaune.
Sannan kuma dole ne wanda zai tsaya masa ya gabatar da ingantaccen katin shaida da kuma hotunan fasfo uku.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Alkalin kotun ta dage cigaba da sauraron karar har zuwa ranar 12 ga watan Janairu na shekarar 2022.