Wata kotun majistare da ke Kano, a ranar Laraba, ta bayar da umarnin tsare wani mutum mai shekaru 37, Jamilu Ahmed, a gidan gyaran hali bisa laifin dukan kaninsa, Alhassan (30), har lahira. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito
Rundunar ‘yan sandan ta gurfanar da Ahmed, wanda ke zaune a Chediyar Kuda Quarters, Kano, bisa zargin laifin kisan kai.
Dan sanda mai gabatar da kara, Aminu Dandago, ya shaida wa kotun cewa Ahmed ya aikata laifin ne a ranar 13 ga watan Fabrairu a Chediyar Kuda Quarters, Kano.
KARANTA WANNAN LABARIN: Bayan Shafe Kwanaki 174, Ƴan Boko Haram Sun Sako Ma’aikacin Agaji
Dandago ya ce a ranar da misalin karfe 10 na dare Ahmed ya yi ta bugun kanin nasa bisa samun sabani da rashin fahimtar juna
Ya kuma ce kanin ya samu raunuka a ciki kuma an kai shi Asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano, inda a nan ne aka tabbatar da ya rasu.
Alkalin kotun, Farouk Ibrahim-Umar, wanda bai amsa rokon Ahmed ba, ya umurci ‘yan sanda da su mayar da kundun bayanan karar zuwa ga daraktan shigar da kararrakin jama’a (DPP) domin neman shawara.
Sannan daga bisani ya dage sauraron karar zuwa ranar 8 ga watan Satumba.
A WANI LABARI KUMA: An yi arangama tsakanin Ɗalibai da Jami’an tsaron Shugaban APC Adamu
A ranar Larabar da ta gabata ne aka yi arangama tsakanin jami’an tsaro da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdulahi Adamu da mambobin kungiyar dalibai ta kasa (NANS).
Sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa ta zama fagen daga inda ‘yan sanda suka harba barkonon tsohuwa mai sa hawaye domin tarwatsa fusatattun mambobin NANS, inda suka tura ma’aikatan sakatariyar da sauran jama’a domin su yi musu zagon kasa