By Abbas Yakubu Yaura
Wata kotun majistare dake zamanta a Ikejan jihar Legas a ranar Talatar data gabata tace an tsare wani yaro dan shekara 14 (wanda aka sakaya sunansa) a gidan gyaran hali bisa zargin yin lalata da wata yarinya ‘yar shekara 13.
Alkalin kotun, O.A Layinka, wanda bata karbi karar matashin ba, ta umurci ‘yan sanda dasu aika fayil din karar zuwa ga daraktan shigar da kararrakin jama’a (DPP) na jihar domin samun shawarar lauya.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa alkalin kotun ta dage cigaba da sauraron karar har zuwa ranar 12 ga watan Janairun sabuwar shekara 2022, zuwa lokacin da zata karbi shawarar lauya daga ofishin DPP.
Lauyan masu shigar da kara, Insp Lucky Ihiehie, ya shaida wa kotun cewa matashin ya aikata laifin ne a ranar 27 ga watan Oktoba a Ogba, jihar Legas.inda yace yaron karami ne wanda ya yi lalata da yarinyar ‘yar shekara 13.
Laifin, a cewarsa, ya sabawa tanadin sashe na 137 na dokar laifuka ta jihar Legas, na shekarar 2015.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa sashin ya tanadi daurin rai da rai saboda lafin aikata fyade.