By Abbas Yakubu Yaura
Wata kotun majistare da ke da mazauni a Akure a jihar Ondo, ta bayar da umarnin a tsare wata mata ‘yar shekara 25 mai suna Rebecca Nicodemus bisa zarginta da daba wa kishiyarta Precious Nikodemus wuka inda ta kasheta har lahira.
An ce wadda ake zargin ta aikata laifin ne a gidan mijinta da ke kauyen Idogun a Ode Irele, hedikwatar karamar hukumar Irele ta jihar a ranar 4 ga watan Fabrairu, 2022.
An tattaro cewa rikicin ya fara ne a lokacin da wanda ake kara, wadda karamar matar ce ta ji cewa mijin nasu ya fi kula da babbar matar (marigayi) fiye da ita.
A ranar da kaddarar ta faru, wai ta fuskanci marigayiyar, a lokacin da ta fito daga dakin da ta kwanta da mijin nasu, sai gardama ta kaure a tsakaninsu, a fusace, wanda ake zargin ta daba wa marigayin wuka wanda haka yayi sanadiyyar mutuwar ta har lahira.
A yayin da ake ci gaba da shari’ar, dan sanda mai shigar da kara, Obadasa Ajiboye, ya shaida wa kotun cewa wadda ake zargin ta kashe marigayiyar ne ta hanyar daba mata wuka a bayanta na hagu wanda ya yi sanadin mutuwarta.
Ya ce wanda ake zargin ta aikata laifin ne da karfe 5 na safe a sansanin Idogun ta Ode-Irele a jihar Ondo.
A cewar mai gabatar da kara, wanda ake tuhuma ta aikata laifin da ya sabawa sashe na 316 da 319 na kundin laifuffuka na 37, 1, na Dokokin Jihar Ondo ta Najeriya, shekarar 2006.
Sai dai wadda ake zargin ta ce ba ta aikata laifin ba amma kotun ba ta amsa karar ta ba.
Lauyan mai gabatar da kara ya gabatar da bukatar ta baka na a daure wanda ake kara a gidan yari har sai an kammala shawarwarin ofishin daraktan kararrakin jama’a.
A hukuncin da ya yanke, Alkalin Kotun Mai shari’a Damilola Sekoni, ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake kara a hannun ‘yan sanda tare da dage shari’ar zuwa ranar 22 ga watan Fabrairun 2022, domin yanke hukunci kan bukatar da a ke yi.