Wata kotun majistare da ke Badagry da ke Legas, a ranar Litinin, ta bayar da umarnin a tsare wani matashi dan shekara 21, Mai suna Tobi David, bisa laifin lalata da wata yarinya ‘yar shekara shida.
Alkalin kotun, Patrick Adekomaiya, wanda bai amsa rokon David ba, ya bayar da umarnin a tsare shi a gidan yari na Kirikri sannan kuma ya umurci ‘yan sanda da su aika da takardar karar zuwa ga daraktan karban kararrakin jama’a (DPP) na jihar, domin neman shawara kafin daga bisani a dage shari’ar zuwa watan 6 ga yunin shekarar, 2022.
Tun da farko, dan sanda mai shigar da kara, ASP Nkem Uko, ya shaida wa kotun cewa David ya aikata laifin ne a ranar 13 ga watan Afrilu da misalin karfe 10 na safe a Ashipa Quarters da ke unguwar Sème a Legas, ta hanyar shigar da yarinyar cikin dakinsa tare da yin lalata da ita.
Mai gabatar da kara ya kara da cewa karamar yarinya tana karbar magani a asibiti. (NAN).
A wani labarin Kuma na daban.
Wani dan kasuwa mai shekaru 34, Cyprian Ebenezer, a ranar Litinin ya gurfana a gaban wata kotun majistare da ke Ikeja, Legas, bisa zarginsa da raunata matarsa da adda.
‘Yan sanda sun tuhumi Ebenezer, wanda ke zaune a Oke-Odo, Legas, da laifin kai hari tare da haddasa munanan raunuka a jikin matar sa.
Lauyan mai shigar da kara, DSP Kehinde Ajayi, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne a ranar 16 ga watan Afrilu a adireshin da aka ambata a sama.
Ta yi zargin cewa wanda ake kara da misalin karfe 11:30 na dare ya lakadawa matar tasa Ruth duka a ido.
Rundunar ‘yan sandan ta kuma ce wanda ake tuhumar ya yi amfani da adda a kan matarsa, inda ya yi mata munanan raunuka a jikinta.
Mai gabatar da kara ya ce laifin ya ci karo da tanadin sashe na 173 da 245 na dokokin aikata laifuka na jihar Legas, na shekarar 2015.
Wanda ake tuhumar ya musanta zargin aikata laifin.
Alkalin kotun Majistare Ejiro Kubeinje ya danka wanda ake tuhumar a hannun beli a kan kudi Naira 100,000 da kuma mutane biyu da za su tsaya masa.
Alkalin kotun ya bada umarnin cewa wadanda za su tsaya masa dole ne su kasance da shaidar biyan haraji, a tantance adireshi sannan daya daga cikin wadanda za su tsaya masa ya zama makusancin sa na jini.
Kubeinje ya dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 31 ga watan Mayu domin cigaba da sauraren karar.
(NAN)