Wata Kotun Majistare da ke Ado-Ekiti a ranar Laraba, ta tasa keyar Adebayo Sunday da Okeowo Obafemi zuwa gidan yari da ke Ado-Ekiti, bisa zargin kasancewa mambobin kungiyar asiri.
Wadanda ake tuhumar, wadanda dukkannin su ‘yan shekara 22 ne, suna fuskantar tuhuma kan zargin kasancewa cikin wata al’umma da ba ta dace ba.
Alkalin kotun mai shari’a Mojisola Salau, wacce ba ta amsa rokon wadanda ake kara ba, ta bayar da umarnin tsare su a gidan yari, har zuwa lokacin da ofishin daraktan shigar da kara na jihar, ya ba da shawara.
Ta kuma dage sauraron karar har zuwa ranar 15 ga watan Disamban shekarar nan.
Tun da farko, Dan sanda mai shigar da kara Sajet Sodiq Adeniyi ya shaidawa kotun cewa wadanda ake tuhumar sun aikata laifin ne a ranar 26 ga watan Nuwamba a garin Ado-Ekiti.
Ya ce wadanda ake tuhumar ‘yan kungiyar asiri ne da ake kira da “Eiye confraternity”.
Adeniyi ya ce laifukan sun ci karo da sashe na 2 na dokar kawar da Yan Kungiyar asiri da haramta aiyukansu, ta shekarar 2017.
Mai gabatar da kara ya bukaci kotun da ta ci gaba da tsare wadanda ake kara a gidan gyaran hali, har zuwa lokacin da Daraktan shigar da kara na jihar(DPP) ya bayar da shawarar ga lauyoyi.