A ranar Alhamis ne aka gabatar da wasu matasa biyu a gaban kotun majastare da ke Kaduna, ana tuhumar su da laifin fashi da makami, daga nan ne alkalin kotun ya umarci a wuce dasu tare da kuma kulle su a gidan yarin Kaduna har sai an samu cikkaken shawara daga ofishin mai gabatar da kara na jihar don sanin irin tuhumar da za a yi musu.
Wadanda ake tuhuma sun hada da Shehu Idris, 32 da Salisu Yusuf, 28, dukkansu mazauna layin Maiduguri da ke Kaduna, ana kuma tuhumar su ne da fashi da makami da kuma mallakar muggan makamai.
Alkalin kotun Ibrahim Emmanuel, bai tsaya sauraron bayani daga wadanda ake tuhumar ba, nan take ya umarci a wuce dasu gidan yari har sai an samu shawara daga ofishin mai gabata da kara na jihar don bayar shawarar yadda za a fuskanci shari’a, daga nan kuma ya daga karar zuwa ranar 25 ga watan Maris don cigaba da sauraron shari’a.
Tun da farko, mai gabatar da karar, Insp. Chidi Leo, ya bayyana wa kotun cewa, wadanda ake zargin sun aikata laifin ne a ranar 23 ga watan Fabrairu a layin Arochukwu a Kaduna.
Ya kuma ce, wadanda ake zargin dauke da muggan makamai sun yi wa wani mai suna Farouq Haruna, fashin kayansa da aka kiyasta kudin su ya kai N8,000 da kuma kudi N15,000.
Ya kuma bayyana cewa, laifin ya sabawa sashi 297 da 299 na dokokin fanel kot na shekarar 2017.