By Abbas Yakubu Yaura
Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa, a ranar Juma’a, ta wanke tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan wanda hakan ya bashi damar tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.
Wannan ci gaban dai na zuwa ne sa’o’i kadan ga bannin gudanar da zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar PDP da aka shirya gudanarwa ranar Asabar a Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kudan Zuma Sunyi Sanadiyyar Mutuwar Wani Yaro Dan Shekara 13 A Jihar Kano
Idan dai za a iya tunawa dai a kwanakin baya ne aka alakanta tsohon shugaban kasar da takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC bayan da kungiyar Fulani ta sayi fom din Naira miliyan 100 a madadinsa.
Sai dai kuma an sha samun matsaya daban-daban kan cancantarsa a zaben shugaban kasa na 2023.
Sai dai a ranar Juma’a, kotun ta ce Jonathan, wanda ya sha kaye a zaben shekarar 2015 a hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari, zai iya tsayawa takara mafi girma a siyasance a kasar.
Alkalin kotun, Mai shari’a Isa Hamma Dashen, wanda ya yanke hukuncin a ranar Juma’a, ya kuma ce ba za a iya dakatar da ‘yancin Jonathan na tsayawa takarar shugabancin kasa a 2023 ba da wata doka ta sake dawowa.
A cikin sammacin asali da Andy Solomon da Idibiye Abraham suka shigar, masu shigar da kara sun nemi kotu ta ba su umarnin cewa Jonathan bai shafe shi ba a karo na hudu da aka yi wa kundin tsarin mulkin kasar na haramtawa mataimakan shugabanin kasa damar yin cikakken wa’adi fiye da daya.
APC, Jonathan da kuma Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa an sanya sunayen wadanda ake tuhuma a kara mai lamba FHC/YNG/CS/86/2022 da ke gaban Mai Shari’a Isa Dashen.
Comments 1