Wata babbar kotun jihar Akwa Ibom da ke zamanta a Uyo, a ranar Juma’ar nan, ta yanke wa wani Basaraken Kauye mai suna Efen Ibom, a karamar hukumar Ika, mai shekaru 82, Cif Essien Matthew Odiong, hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsa da laifin kisan kai.
Wanda aka yanke wa hukuncin, yana auren mata 12 da ‘ya’ya 60, yana fuskantar shari’a bisa tuhume-tuhume hudu da suka hada da hada baki, da jagorantar shari’ar da ba ta dace ba ta hanyar azabtarwa, satar babur da kuma kashe mai gida, dan unguwarsu, Udoma Akpan Udo Ubom.
A hukuncin da ta yanke, kotun da Mai shari’a Edem Akpan ya jagoranta, ta samu wanda ake tuhuma da laifin kashe Udoma Akpan Udo Ubom ta hanyar allurar wani sinadari wanda ya kai ga mutuwarsa a ranar 26 ga watan Afrilu, na shekarar 2017.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, ‘Yan uwansa sun tuhumi marigayi Ubom da cewa matsafi ne, inda suka kai rahoto ga Hakimin Kauyen, wanda ya kai shi gaban Majalisar Efen, inda marigayin ya rantse cewa shi ba mayen ba ne.
KARANTA WANNAN: https://dimokuradiyya.com.ng/%c6%b4an-%c6%99ungiyar-asiri-sun-hallaka-mutane-biyu-a-bayelsa/
Kotun ta ce “bayan ya fahimci sakamakon laifin da ya aikatawa murgayin, sarkin ya tsere daga kauyen a shekarar 2017 ya dawo a 2019, lokacin da ‘yan sanda suka kama shi.”
Mai shari’a Akpan ya kuma ce tun da “wanda ake tuhumar ya amince da radin kansa cewa ya zauna a Efen Clan Council tare da wasu shugabannin kauyuka biyar da kuma ‘yan majalisar Clan domin yi wa marigayin shari’a kan zargin maita, doka ta sassauta tuhumar da ake yi masa ya tabbatar da laifin makirci”.
Kotun ta ci gaba da cewa, “Sanarwar da aka yi na shari’ar da kuma hukuncin da kungiyar ‘yan kabilar Efen ta yanke na yin rantsuwa a kan marigayin ya sa aka yi amfani da wani wankan roba da aka yi akan marigayi Udoma Akpan Udo Ubom tare da yi masa allurar wani sinadarin wani abu ta hanyar sirinji da shugaban kauyen ya yi masa a gabansa ‘gindinsa’, ya yi sanadiyyar mutuwar marigayin.”
Mai shari’a Akpan ya yanke wa Hakimin Kauyen hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsa da laifin kisan kai, daurin shekara bakwai a gidan yari tare da aiki tukuru saboda ya jagoranci shari’ar da ba bisa ka’ida ba ta hanyar wahala da kuma daurin shekaru uku a gidan yari bisa laifin hada baki da wasu.
Channels TV