Wata kotun Majistret dake Sokoto ta yanke ma Emmanuel Bassey tare da matar sa Esther Emmanual hukunci shekara uku gidan kaso, biyo bayan kulle Yarinyar su mai kimanin shekaru 12 a cikin firiza har na tsawon wata takwas. Kamar yadda Jaridar Tvcnews ta wallafa a shafinta
Mai shari’ar Shuaibu Ahmad, ya kuma sanya musu tarar dubu ashirin da biyar kan wannan mummunan aikin da sukayi.
Sannan ya kara saka musu tarar dubu dari biyu da saba’in da biyar.
KARANTA:- Aminu Waziri Tambuwal ya sha alwashin kara himma wajan tabbatar da lafiya a Jahar Sokoto
Yace an kama ma’auratan dumu dumu da laifin, ya kuma Kara musu zaman gidan kaso na wata sha biyu da kuma tara naira dari, tun da farko dai an yake musu hukunci shekara uku gidan kaso.
Mai shari’ar yace za su fara zaman gidan kasonne nan take.
Ya Kuma baiwa Goodness Emmanuel da Happiness Emmanuel yaran Emmanuel Bassey beli akan 500,000 ko wannen su.
Jaridar Tvcnews ta ruwaito a watan May, 2021, cewar an sanya wata yarinya mai kimanin shekaru sha biyu a cikin firiza.
A dai lokacin makotansu suka kai rohoto ga jami’an Yan sanda aka kubutar da Yarinyar, sannan aka kama wadanda suka aikata laifin.
A wani labarin
Bankin duniya ya jinjinawa Yahaya Bello baya loda wasu makudan kudade
Gwamnan Jahar Kogi Yahaya Bello ya sami lambar yabo daga babban bankin duniya bayan ya zuba kudade dala milyan 4.63.
Babban bankin duniya ya nuna jindadinsa baya saka makudan kudaden da ya samar karkashin hukumar Nigeria Erosion and Watershed Management Project (NEWMAP).
A wani sakon takadda wanda Shugaban bankin Shubham Chaudhari ya nuna cewa wannan salon mulkin adalci ne.
Kamar yadda bankin duniya ya bayyana ya kara tsawaita damar kulla Yarjejeniya kan wasu ayyukan na daban da sauran wasu jahohi biyo bayan babbab abunda gwamna Yahaya Bello yayi.
Kamar yadda jawabin ya kunsa a takardar ” “Na rubutu wannan sako ne don nuna jindadina bisa makudan kudaden da ka turo zuwa reshen Plateu na dala miliyan 4.63.”
“Bisa wannan gagarumar aiki ka sanya bankin tsawaita wa’adin rufe kulla Yarjejeniya kan wasu ayyukan daga 30 June 2021 zuwa 30 June 2022. Wannan na nuna mulki na adalci da gwamnatin ka take gudanarwa.”
“Zuba kudaden ya saura jahohi dake da bukatar kammala sauran ayyukansu su kammala, sannan Kuma Jahar Kogi na kokarin cigaba da sauran ayyukansu.”
“Za kuma mu cigaba da wai-waiyen gwamnatin ka don ganin ka kammala sauran ayyukan naka.”
“Muna yin amfani da wannan dama wajan mika godiyan mu da jindadin fatan wannan sako zai kara maka kaimi.”