By Ishaq Dabai
A ranar Laraba ne wata Babbar Kotu a Maiduguri ta yanke wa dalibai 19 hukuncin daurin shekaru shida kowannen su saboda aikata laifin shiga kungiyar asiri.
Da yake yanke hukunci, Mai shari’a Umar Fadawu, yace akwai isassun shaidun dake tabbatar da cewa kowanne daga cikin wadanda ake tuhuma ya aikata laifin kulla makirci da gudanarwa zama memba na haramtacciyar al’umma.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa ‘yan sanda sun kama wadanda aka yanke wa hukuncin a ranar 21 ga watan Satumba na shekarar 2019 a wani otal a Maiduguri saboda kasancewar su ‘yan wata haramtacciyar al’umma, (Neo Black Movement a. k. a Black)
Faduwu bayan duba rokon wasu daga cikin wadanda aka yankewa hukunci da lauyansu, Mista Ahmed Hamman,yayi wanda ya roki a yi masu sassauci, ya yanke wa wadanda aka yanke wa hukuncin daurin shekaru shida kowannensu a kan laifuka biyu ba tare da zabin biyan tara ba.
“Kotu ta yanke muku hukuncin dauri inda suka hadar da Arnold Augustine, Onu Chiduben, David Emmanuel, Awuto Abayomi, Mustapha Abulkadir, Levi Epraim, Onuebu Godspower Chibuzor, Ben Oni, Yakubu Chiroma, Mohammed Adamu, Calvin Ijafiya, Henry Michael Ujah, Chris Kallu, Totsi Samuel, Onwuka Ugochukwu, Audi Yohana, Samuel Talba, Donald Omguze da Joseph Olaiya zuwa gidan yari na shekaru shida akan kowanne laifi.
Fadawu ya yanke hukuncin cewa “zaman gidan yari zai gudana lokaci guda daga yau, 20 ga Oktoba.”