By Abbas Yakubu Yaura
A kasar Mauritius wata kotu ta yanke hukuncin daurin watanni 20 ga wani kyaftin din jirgi kuma abokin zama na farko na MW Wakashio, biyo bayan nutsewar wani jirgin dakon mai a shekarar 2020 wanda ya haifar da malalar mai mafi muni a gabar tekun Mauritius.
Alkalin kotun ya kara da cewa dukkan wadanda ake tuhumar sun amsa laifinsu tare da basu hakuri.
Jirgin ruwan kasar Japan ya yi kasa ya nutse a ranar 25 ga watan Yulin shekarar 2020 a gabar tekun murjani kudu maso gabashin kasar Mauritius, inda ya saki sama da tan 1,000 na man a cikin ruwan sa mai haske.
Jirgin ruwan mai dauke da tutar kasar Panama yana kan hanyarsa ta zuwa kasar Brazil daga Singapore dauke da tan 3,800 na man fetur da kuma tan 200 na dizal, wanda nan da nan ya fara kwararowa amma galibi ana iya fitar da su.
A yayin sauraron karar, Kyaftin din Indiya, Sunil Kumar Nandeshwar, ya amince cewa yana shan giya a wurin wani liyafa a cikin jirgin.
Zubewar man dai ita ce gurbacewar ruwa mafi muni a tarihin kasar, wanda ta dogara da ruwanta wajen samar da abinci da kuma yawon bude ido, a wani yanki da ke da kyawawan kogin murjani a duniya.