Wata babbar kotun jihar Oyo da ke zamanta a Ibadan babban birnin jihar Oyo ta yankewa wasu masu damfara ta yanar gizo akalla sittin da shida (66) hukuncin dauri daban-daban da gidan yari.
Daily Post ta ruwaito cewa, Hukuncin daurin ya kai daga sati biyu, wata hudu da wata shida na yiwa al’umma hidima zuwa wata goma a gidan yari.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Tsinci Gawar Lauyan Da Kotun ICC Ke Tuhuma A Kenya
Hukuncin da aka yiwa masu damfarar yanar gizo ya biyo bayan kamasu ne da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta yi.
A baya dai hukumar EFCC ta kama wadanda ake zargin wadanda a halin yanzu aka yanke musu hukunci kan aika laifukan zamba daban-daban, .
Tun da farko dai hukumar EFCC shiyyar Ibadan ce ta gurfanar da wadanda ake tuhumar.
Masu damfarar ta yanar gizo kamar yadda Wilson Uwujaren, shugaban yada labarai da yada labarai na EFCC ya bayyana an gurfanar da su a gaban mai shari’a Olusola Adetujoye, Bayo Taiwo da Ladiran Akintola bisa wasu tuhume-tuhume da suka shafi laifukan zamba ta yanar gizo, tsakanin Litinin, 5 ga Satumba, 2022, da ranar Laraba 21 ga Satumba shekarar 2022.
Uwujaren, a wata sanarwa da ya raba wa DAILY POST a ranar Talata, ya ce wadanda aka yanke wa hukuncin sun hada da; Lawal Ismaila Adebola, Dazumi Azeez Jayeola, Morakinyo Abiodun Michael, Kehinde Samuel Olatunbosun, Yusuf Olawale Raji, Abass Akintayo Waliu, Kolawole Blessing Oluwafemi, Ajibade Habib Olakunle, Adedun Olajide Temidire, Dapo Ajayi Temitope Faith, Lami Patrick Olamide, Simoni Patrick Olamide, Lami Patrick Olamide Nurudeen, Obaloluwa Enoch Bolaji, Oladimeji Olamide Abdulrahman, Damilola Mubarak Muritala, Adedayo Wahab Abdullahi, Olotu Oluwadamilola Ayomikun, Aderibigbe Ibrahim Olamilekan, Sekoni Oluwatimilehin James, Dazumi Abdulrazak, Salami Ayo Wisdom da Ifeoluwa Joseph Olabiyi.
Sauran sun hada da Mubarak Salaudeen Opeyemi, Toriola Samuel Oluwadamilola, Abisoye Israel Olamilekan, Adebayo Babatunde Teslim, Onipede Damilola, Oladotun Tijani Kunle, Adeshina Opeyemi Akanni, Eniola Johnson Olorunsola, Adebowale Samuel Amusan, Ayinde Babalola Quadri, Obiochi Tomi Honor Nolami Afeni Opeyemi Saheed, Adekunle Hammed, Abioye Oluwatobiloba Alex, Ajadi Hezekiah Oluwatobi, Kayode Donald Adubu, Olamilekan Gabriel Ebedi, Adediran Qudus Wale, Adams Ojo Segun, Ogundayo Usman Oladayo, Olamide Yusuf Ishola, Kolawole Fuad Abiodun, Adekoya Tobitunde, David Babafata, Giwa Babafata Dolapo Oderinde da Akinwale Israel Bunmi.
Sauran su ne; Alex Okhiria Chibueze, Gabriel Ikyeleve, Paul Uche Obinna, Udeh Emeka Moses, Alase Ayodele Philip, Afeez Sode Gbolahan, Abayomi Babatunde Adejuyigbe, Haruna Adedoyin Kayode, Adejuyigbe Oluwatobiloba Joshua, Gbadamosi Samson Iyanu, Olatunbosun Mojeeb Olanrewaye Afisale Kelfeez, Olfeez, Olatunbosun , Emmanuel Oluwatobi Ajala, Olamilekan Michael Ayegbusi da kuma Adurota Emmanuel Oluwatosin.
Uwujaren, a cikin sanarwar, ya kara da cewa wadanda aka yankewa hukuncin, duk sun amsa laifin da ake tuhumar su da su a lokacin da aka karanta musu su a gaban Kotun .
Lauyoyin masu gabatar da kara, Oyelakin Oyediran, Chidebere Okoli, Oluwatoyin Owodunni, Modupe Akunkoye, Mohammed Galadanchi, Mabas Mabur, Abdulrasheed Suleman da Samsudeen Bashir, sun roki kotun da ta yanke wa mutanen hukunci dai dai da abun da suka aikata..
Daga nan ne kotuna ta yanke wa wadanda ake tuhuma hukuncin dauri daban-daban a gidan yari.
Wasu daga cikin masu damfarar ta yanar gizo zasu kwashe daure makwanni biyu a gidan yari yayin da wasu kuma na su ya kai daure watanni hudu.
Wasu kuma an yanke musu hukuncin daurin watanni shida na aikin yiwa al’umma hidima, yayin da wasu kuma aka yanke musu hukuncin daurin watanni goma a gidan yari.
Kotun bayan ta yanke musu hukuncin, ta kuma ba da umarnin a mayar da dukkan kayayyakin da aka kwato daga hannunsu ga gwamnatin Tarayya .
A WANI LABARIN KUMA: Sojoji Sun Kubutar Da Uwa Da ‘Ya’yanta A Kaduna
Dakarun rundunar ‘Operation Forest Sanity’ sun ceto wata uwa da aka yi garkuwa da ‘ya’yanta hudu tare da wasu mutanen kauyen uku a wani sintiri a kananan hukumomin Birnin Gwari da Chikun.
Daily Trust ta ruwaito cewa sojojin sun fuskanci luguden wuta daga ‘yan bindigar a lokacin da suke sintiri a kan titin Birnin Gwari-Gyam-Kuriga-Manini.