Kotu Ta Yankewa Wani Mai Shekaru 65 Hukuncin Gidan Kaso
Mai Shari’a Musa Ubale dake Babbar kotu mai lamba 6. Birnin Kudu a Jigawa ta yankewa Abiu Suleliman mai shekaru 65 Hukuncin zaman gidan kaso har abada kan yiwa wani yaro mai shekaru 15 fyade yaron dake garin kiyawa, Karamar Hukumar Kiyawa a cikin jahar Jigawa.
KARANTA:-Wani ya kashe matar shi a Benin, sabida Naira 2,000
Bayan sauraran dalilai daga bakin wadan masu kara sun gabatar da hujjoji gamsassu guda hudu, Alkalin ya tabbatar da laifin shi sannan ya yanke masa hukuncin zaman gidan kaso na dindindin.
A wani sanarwa da aka fidda ta kafafen yada labarai wadda mai kula da huldodin jama’a a fagen Shari’a Zainab Baba Santali tace Alkalin yace hakan zai zama aya ga wanda ya aikata laifin.
A wani bangaren, ranar sha takwasga watan Yuni wata Kotu dake kano ta yanke hukunci tsakanin Samaila Bello da gwamantin Jahar No: CA/K/637/C/18. lamba No JDU/1c/2010, in da kotun ta yankewa Samaila Bello hukuncin Kisa kan hadakai da Yan ta’adda da Kuma fashi da makami.
Wanda ya Jagoranci Kotun Alkalin Hussain A. Muktar PJCA, ya hana bada beli akan sa, ya tsaya kan hukuncin da kotu ta yanke masa kan zaman gidan kaso na har abada.