Kotun masana’antu ta kasa, NIC, ta yi sammacin gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, da su gurfana a gabanta a ranar Litinin a Abuja, kan yajin aikin da kungiyar ta shiga tsahon watanni takwas da suka gabata.
Wannan sammacin na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin tarayya ta yanke shawarar mika takaddamar da ta ki ci ta ki cinyewa a tsakaninta da ASUU ga kotun NIC.
Karanta kuma: Gwamnatin Tarayya Ta Maka ASUU A Gaban Kotu Kan Yajin Aiki
Gwamnatin tarayya na neman kotu da ta umarci ASUU ta koma harkokin ilimi, bayan rufe jami’o’in gwamnati na tsawon watanni takwas.
Jaridar Daily Post ta rawaito cewa, Wasikar sammacin da kotun ta bayar a ranar 9 ga watan Satumba mai dauke da sa hannun babban magatakarda ta nuna cewa zaman kotun masana’antu ta kasa zai kasance a gini mai lamba 11, New-Bussa close, Area 3, Garki Abuja, a ranar Litinin 12 ga Satumba, 2022, da karfe 9 na safe.
A wani labarin kuma: Hukumar Tsaro DSS Ta Mayar Da Martani Kan Zargin Da Gumi Ya Yi
Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta ce sakamakon binciken da ta gudanar a kan Tukur Mamu abin damuwa ne.
Ga dukkan alamu da ta ke mayar da martani kan kalaman malamin addinin musuluncin nan na Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce hukumar ba za ta hankalta ba.