Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Alhamis ta yi watsi da karar da jam’iyyar adawa ta PDP ta shigar a kan gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrasaq, kan mallakar takardar shedar kammala karatu na bogi.
Mai shari’a Inyang Edem Ekwo, yayin da ya yi watsi da karar, ya ce shari’ar PDP ba ta da tushe balle makama kuma ta zama babban cin zarafi ga kotu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dubu Ta Cika: An Kama Kwamishinan Yan Sandan Bogi da Ya Damfari Wani Miliyan N250m
Jam’iyyar PDP ta kai karar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, Abdulrahman Abdulrasaq da jam’iyyar APC a matsayin wadanda ake kara na 1 zuwa 3.
A cikin karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1324/2022, PDP ta yi rokon a haramtawa Gwamna da APC zaben gwamna a 2023 bisa zargin gabatar da takardar shaidar kammala jarabawar WAEC ta jabu domin samun tikitin tsayawa takara.
Jam’iyyar ta kuma yi t
rokon a ba da umarnin Kotu ta tilasta wa INEC ta cire sunan Gwamnan da APC daga cikin wadanda aka wanke domin gudanar da babban zabe.
Sai dai a hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Ekwo ya amince da matakin farko na kin amincewa da karar da wani Babban Lauyan Najeriya (SAN), Prince Lateef Olasunkanmi Fagbemi ya shigar a madadin Gwamnan.
Alkalin kotun ya amince da Fagbemi cewa takardar shedar jabu da shaidar zur ta fito ne a wata kara a shekarar 2019 daga hannun tsohon dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, Rasaki Atunwa, wanda mai shari’a Bassey Effiong Ikpeme ya yanke hukunci tare da korar sa saboda rashin kima da rashin cancanta.
Mai shari’a Ekwo ya bayyana cewa jam’iyyar PDP ba ta da wurin da ake bukata domin kalubalantar zaben fidda gwani da ya samar da Abdulrasaq a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar APC saboda ba shi ne dan takara a zaben fidda gwani ba.
Alkalin ya kuma amince da Fagbemi cewa PDP ta kasance mai shagaltuwa kuma mai shiga tsakani domin ba ta da hurumin yin kutse a cikin harkokin cikin gida na jam’iyyar APC.
A cewar mai shari’a, karar jam’iyyar PDP ta bayyana babu wani dalili mai ma’ana da za ta dauka saboda an duba takardar shaidar jabu da aka yi watsi da ita tun a shekarar 2019.
Baya ga haka, Mai shari’a Ekwo ya ce karar ba ta da rai da za ta dore da ita ko kuma kafafun da za su tsaya a kan lokacin da doka ta tanada.
“Da zarar kotu ta gamsu da shari’ar da ke gabanta ya kai ga cin zarafi, to a gaskiya kotu tana da hakkin yin amfani da ikonta na tilastawa ta hukunta jam’iyyar da ke cin zarafin tsarinta.
“Irin wannan iko sau da yawa ana amfani da shi ta hanyar watsi da matakin da ya haifar da cin zarafi. Don haka na ba da umarnin yin watsi da wannan shari’ar saboda cin zarafi na kotu,” inji Alkalin.
Babban Lauyan Najeriya SAN, Cif Paul Erokoro ne ya shigar da karar a madadin PDP.
An bukaci kotun da ta yi amfani da sashe na 171 da 285 na kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 1999 da kuma sashe na 29 na dokar zabe domin soke shirin da gwamnan zai yi a zabe mai zuwa.
Babban abin da jam’iyyar ta sa a gaba shi ne cewa takardar shaidar WAEC da Gwamna ya mika ta hannun jam’iyyar APC ga INEC da kuma cancantarsa na ilimi kamar yadda sashe na 177 na kundin tsarin mulkin 1999 ya yi na jabu ne ba nasa ba.
A wani labarin kuma, Shugaba Buhari Ya Yi Allah-Wadai Da Hallaka Jami’an NSCDC 7 a Kaduna
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da kashe jami’an hukumar tsaro ta farin kaya NSCDC guda bakwai da ‘yan bindiga suka yi musu kwanton bauna a jihar Kaduna a lokacin da suke bakin aiki.
A cewar wata sanarwa da Garba Shehu, babban mai taimaka wa shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai, ya fitar a ranar Alhamis, yayin da yake bayyana alhininsa game da rasuwar, shugaban ya bayyana rashin jami’an NSCDC a matsayin wani lamari mai ban tausayi tare da jinjinawa jajircewar mutanen da suka sadaukar da rayukansu ga al’umma.