Wani mutum mai shekaru 35, Badung David Dele, ya tabbatar da cewa, shi ne ya kashe budurwarsa, Nanchin Zakaria, a ranar masoya ta 2016 a Jos, jihar Filato, wanda hakan ya sa kotu ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.
A jiya ne mai shari’a Arum Ashom na babbar kotun Jos ya yanke hukuncin kisan.
Mai shari’a Ashom ya ce kotun ta samu wanda ake zargin da laifin aikata laifin kisan kai wanda ke dauke da hukuncin kisa, hukuncin kisa a karkashin sashe na 221 na kundin laifuffuka, Cap 89, na kundun dokar kasa Najeriya 1963.
A cewar alkalin, “Lauyan mai gabatar da kara ya sauke nauyin da aka dora masa a shari’ar ta hanyar tabbatar da karar sa ba tare da wata shakka ba.
“Wanda ake tuhumar ya kasa kare kan sa, kuma kotu ta gamsu da hujjojin da aka gabatar na cewa wanda ake zargin yana da alhakin mutuwar Nanchin Zakaria a watan Fabrairun 2016.
“Tare da shaidun da ke gaban kotu, wanda ake zargin yana da laifi kamar yadda ake tuhumarsa kuma an yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya. Allah ya jikansa da rahama” inji alkalin kotun.
A wani labarin kuma na daban.
Yawan Sauya Sheka: Jam’iyar APC ta gudanar da taron sulhu a jihar Kebbi
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta fara yunkurin dakatar da ficewar mambobinta zuwa jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Kebbi.
A jiya ne jam’iyyar ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki da aka kira domin sasantawa da ‘ya’yan da aka tsammanin ba’a damawa dasu, domin dakatar da yunkurina su na sauya sheka.
MKwanan nan ne wasu jiga-jigan jam’iyyar APC suka dunguma zuwa PDP saboda wasu dalilai. Jam’iyyar ta rasa Sanata Adamu Aliero da Dokta Yahaya Abdullahi da kuma dan majalisar wakilai, Barista Mohammed Bello Yakubu (Relisco), Mohammed Umar Jega da Abdullahi Zumbo.
‘Yan majalisar dokokin jihar, Habibu Labbo, Ismaila Bui da Mohammed Buhari Aliero, sun fice daga jam’iyyar suma.
Da yake jawabi yayin taron mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa a shiyyar (Arewa maso yamma), Salisu Lukman, ya ce taron an yi shi ne da nufin magance korafe-korafen jiga-jigan jam’iyyar a jihar.
“Duk da sauya sheka da jam’iyyar ta samu, har yanzu ina da kwarin gwiwar cewa APC ce jam’iyyar da za ta lashe zabe a 2023. Ina iya ganin hadin kan ‘ya’yan jam’iyyar na ci gaba da habaka kuma hakan na nuni da samun gagarumar nasara a karshe,” inji shi.
Ya kara da cewa jam’iyyar na bukatar dukkanin mambobin ta da su samu nasara a 2023, inda ya bayyana cewa, an yi taron ne domin jin ta bakin dukkanin ‘ya’yan jam’iiyar, da suka koka don samun mafita a matakin kasa.