A yau Talata ne ake sa ran wata kotu a kasar Guine zata yanke hukunci kan ƙarar da ke gabanta kan yuwuwar bada belin tsohon firaministan kasar da wasu jami’an gwamnatinsa da aka gurfanar akan zargin cin hanci da Rashawa.
Tsohon firaministan kasar Ibrahim Fofana da wasu manyan jami’an gwamnatin da suka yi aiki a gwamnatin tsohon shugaban kasar Alpha Conde an tsare su ne a ranar 6 Afirilu bisa zargin su da almun dahanan dukiyar ƙasa.
Fofana dai ya zama firiministan ƙasar ne daga shekarar 2018 har izuwa lokacin da sojoji suka tumbuke gwamnatin Conde A watan Satumban bara.
A yanzu haka dai ana cigaba da tsare Fofana da tsohon ministan tsaron kasar Mohammed Diane, da tsohon Ministan Muhalli Oye Guilavogui, da na man Fetur a babban gidan yarin kasar dake babban birnin ƙasar ta Guinea.
A sati da ya gabata ne gwamnatin sojin kasar karkashin jagorancin Mamadi Doumbouya ta sanar da aniyar ta na yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙasar wanda ya haɗa da tsofin jami’an ƙasar.
A wani labarin Kuma na daban.
2023: Allah Kaɗai ne zai zaɓi wanda zai gaje ni — Gwamna Okowa
Gwamnan Jahar Delta Ifeanyi Okowa yace a shirye yake ya baiwa Allah zaɓi ya nuna wanda zai gaje shi a shekarar 2023.
Okowa ya bayyana haka a taron Murnar zagayowar ranar haihuwa da Bada kyaututtuka na Chief Oritsetimeyin Adams a Cocin Cathedral Dake Sapele a Ƙaramar Hukumar Sapele.
Gwamnan yace baya da sha’awar ya baiwa mutane suyi zaɓi, amma ya barwa Allah ya zaɓarwa Jahar Gwamnan daya fishi wanda zai gaje shi.
Ya yabawa Cocin da Sauran Shuwagabannin ta da addu’o’i da goyon baya, sai yayi addu’a ga Allah daya zaɓarwa Jahar Gwamnan daya fi cancanta wanda zai gaje shi.
“Zaɓar wanda zai gaje Ni bawai zaɓi na bane ba, amma zaɓin Allah ne.
“Ina addu’a duk wanda Allah yake so ya zama Gwamna, Allah yasa ya zamo ya fini.
Gwamnan ya taya wanda aka shirya wa bikin ranar zagayowar haihuwar daya cimma Shekarun, sai ya buƙace shi daya maida hankali wajen yiwa Allah bauta da Al’umma baki ɗaya.