Kotun Ɗaukaka Ƙara dake zaman ta a Lagos ta kori ɗaukaka ƙarar da tsohuwar Ministar Man Fetur Diezani Alison-Madueke tayi, inda take ƙalubalantar ƙwace mata kayan gwala-gwalai nata da darajar su takai Dala Miliyan $40 zuwa Gwamnatin Tarayya.
Kotun tace babu wani dalili dazai sanya ta rushe hukuncin da ƙaramar kotu ta yanke akan Alison-Madueke.
KARANTA WANNAN LABARIN: Akpabio Ya Ziyarci Tinubu Kan Rugujewar Ginin Ikoyi Na Jihar Legas
Kotun ta kuma tabbatar da cewa hukuncin da aka yanke na shekarar 2019 wanda mai Shari’a Nicholas Oweibo na Babbar Kotun Tarayya wanda ya bada umarnin ƙwace gwala-gwalai, biyo bayan roƙo da Hukumar yaƙi da zagon ƙasa tayi.
Kotun ɗaukaka ƙara ta bada hukuncin ta akan ɗaukaka ƙara da Alison-Madueke ta shigar mai lamba No CA/L/1263/19, tsakanin ta da EFCC.