Kotun Kolin Birtaniya ta yanke hukuncin cewa mazauna yankin Neja Delta dubu 40 a Najeriya na iya gurfanar da kamfanin Shell a kotu domin neman diyya kan gurbata musu muhalli da ya yi a aikin sa na hakar mai.
Hukuncin ya sauya wanda aka yanke a shekarar 2017 a karar da mutane Ogale da Bille suka shigar wadanda suka bukaci biyan diyya kan gurbata musu muhalli da kamfanin ya kwashe shekaru yanayi a yankin mai arzikin mai.
Masu shigar da karar na bukatar ganin anyi shari’ar karar da suka shigar da kamfanin Shell a London saboda ba su da yakinin cewar za a musu adalci a Najeriya.
Wannan hukunci na Birtaniya na zuwa ne makwanni biyu bayan wata kotu a Netherlands ta bukaci kamfanin Shell ya biya mazauna wasu kauyuka biyu diyya bayan kwashe shekaru 13 ana tafka mahawara a kotu.
A hukuncin da suka gabatar yau, alkalan kotun London guda 5 sun bayyana cewar hukuncin da kotun daukaka karar kasar ta gabatar kuskure ne, saboda haka sun yi watsi da shi.
Lauyan da ya wakilci masu gabatar da karar Daniel Leader ya bayyana hukuncin na yau a maytsayin gagarumar nasara ga mutanen Ogale da Bille wadanda suka kwashe shekaru suna bukatar kamfanin Shell ya tsaftace musu muhallin da ya gurbata.
Kamfanin Shell ya bayyana hukuncin nay au a matsayin abin takaici, inda ya danganta zubar man da ake samu a yankin ga masu fasa masa bututu suna satar man.