Kotun Daukaka Kara a Kaduna ta kori ‘yan majalisar jihar biyu a zaman da tayi ranar Talata.
Kotun ta yi wa hukumar INEC umurnin ta sake zabe a mazabun Kagarko da na Sanga.
A Kagarko, kotun tayi umurni a sake zabe a rumfuna 22 dake gundumomi biyu.
A cikin shari’ar da Mai Shari’a Daniel Kaliop ya tabbatar da hukuncin da kotun zabe ta yi akan mazabar Kagarko.
Rahoton Kamfanin Dillancin Nijeriya a kwanaki ya yi nuni da cewa Nuhu Shadalafiya na jam’iyyar APC ya kalubalanci nasarar Morondia Tanko na PDP a kotun zabe a ranar 9 ga watan Maris.
Kotun zaben ta yanke hukunci akan a sake zabe a rumfuna 22 amma Tanko na jam’iyyar PDP ya tafi Kotun Daukaka Kara ya na neman tayi watsi da hukuncin Kotun Zabe.
Kotun Daukaka Kara ta yi fatali da bukatun nashi, inda tayi wa hukumar zabe mai zaman kanta umurnin ta sake shirya zabe a rumfuna ashirin da biyun kamar yadda Kotun Zabe tayi umurni a baya.
Lauyan Shadalafiya, Ussy Edikhiola ya ce sun yi farin ciki da wannan hukunci.
Har ila yau, Kotun ta yi umurni da a sake zabe a mazabar Sanga, bayan ta yi watsi da hukuncin Kotun Zabe inda aka ayyana Confort Amwe ta jam’iyyar PDP a matsayin wacce ta yi nasara.
Confort Amwe ita kadai ce mace a majalisar dokokin jihar Kaduna.
Alhaji Gambo Danga na jam’iyyar APC ne ya kalubalanci hukuncin Kotun Zaben a Kotun Daukaka Karar dake zama a Kaduna.