Rahotanni da suka fito daga jihar Sakkwato, sun nuna cewa a jiya Litinin kotun sauraren daukaka kara ta yi watsi da karar da Aminu Shagari da Kabiru Achida na PDP suka shigar gabanta, suna mai kalubalantar zaben Abubakar Yabo da Almustapha Rabah na APC.
Shagari da Achida sun tsaya takara ne a zaben 2019 domin wakiltar Yabo/Shagari da Rabah/Wurno a majalisar tarayya a karkashin jam’iyyar PDP.
Da yake yanke hukunci, Justice Saulawa ya ce kotun ba ta da iko, domin ikon kotun ya kare tun 2 zuwa 3 ga watan Nuwamba.
Sannan har wala yau, kotun daukaka karar ta yi watsi da karar Alhaji Sa’idu Na-Bunkari na APC wanda yake kalubalantar zaben Alhaji Mani Maishinku na PDP mai wakiltar Binji/Silame a majalisar tarayya.