Kotun Kungiyar kasashen Afirka ta Yamma wato ECOWAS ta umurci gwamnatin tarayya da ta biya wasu sojojin kasar 244 da ta kora daga aiki a shekarar 2016 hakkokin su cikin gaggawa, bayan rundunar sojin kasar ta same su da laifin tserewa daga bakin daga a yakin da suke fafatawa da kungiyar Boko Haram.
A hukuncin da ta yanke, kotun ta hannu mai shari’a Keikura Bangura, ta ce korar sojojin daga bakin aiki ya saba ka’ida, saboda haka ta bukaci gwamnatin Nijeriya ta biya su hakkokin su, duk da yake kotun taki amincewa da bukatar mayar da su bakin aiki da suka nemi ta yi.
Kotun ECOWAS ta ce gabatar da korar sojojin daga aiki ba tare da gabatar su a gaban shari’a ba domin yi musu hukunci ya saba ka’ida, saboda haka ta bukaci gwamnati ta biya su kudaden su.
Gidan Rediyon Faransa ya labarto cewa; Alkalai 3 suka saurari karar suka kuma yanke hukunci, cikin su harda Gberi-Be Ouattara da ya jagoranci shari’ar da Dupe Atoki da kuma Keikura Bangura.