Kotun Hukunta manyan laifuffuka ta Majalisar Dinkin Duniya ta fara gudanar da taron ta a New York domin zabo wanda zai maye gurbin Babban Mai Gabatar da kara Fatou Bensouda sakamakon kawo karshen wa’adin aikin ta.
Yanzu haka ‘yan takara 4 dukkan su maza ne ke fafatawa domin maye gurbin Bensouda wadda ta fito daga kasar Gambia ta kuma yi kaurin suna saboda gudanar da bincike kan yakin Afghanistan da rikici tsakanin Israila da Falasdinu wanda ake zargin Israilar da aikata laifuffukan yaki wajen kasha fararen hula a shekarar 2012.
Yan takarar sun fito ne daga kasashen Birtaniya da Ireland da Italia da kuma Spain, amma babu guda daga cikin su da ya samu nasara wajen samun kuri’un da ake bukata a kuri’ar da aka kada yau, amma Karim Khan, lauya ‘dan kasar Birtaniya ke sahun gaba, wajen samun kuri’u 59, yayin da Fergal Gaynor, dan kasar Ireland ya zo na biyu da kuri’u 47.
Khan ya taba tsayawa dan tsohon shugaban Libya Seif Islam a shari’ar da ake masa, yayin da Gaynor kuma ya taba wakiltar mutanen da aka cin zarafin su a yakin Afghanistan a gaban kotun da kuma wata shari’ar da ta shafi shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta.