ganduje 2

Kotun Koli Ta Tabbatar Da Nasarar Ganduje

Kotun Kolin Nijeriya ta kori karar Abba Kabir Yusuf inda ta tabbatar wa Abdullahi Umar Ganduje da kujerarsa.

Shari’ar farko da aka fara kira a wannan rana ita ce tsakanin Abba Kabir Yusuf da wadanda yake kara bangarori biyu, Ganduje da hukumar INEC. Inda aka fara karanta hukunci.

Wannan shari’a ta Kano ta dauki hankalin al’umma, watakila saboda irin sarkakiyar da ke cikinta da kuma girman jihar a matsayinta nta cibiyar kasuwanci ta arewacin Nijeriya.

Yanke wannan hukunci ke da wuya sai mabiyan Ganduje da Abba suka fara barin cikin Kotun Kolin, in ji majiyarmu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *