By Abbas Yakubu Yaura
A ranar Talata ne kotun kolin kasar Kenya ta fara sauraren wani kudurin dokar sake duba kundin tsarin mulkin kasar mai cike da cece-kuce da aka kwashe shekaru da dama ana yi a kasar da ke gabashin Afirka.
Wanda aka fi sani da (BBI), wannan bita na shirin samar da sabbin mukamai a bangaren zartarwa (firaminista, mataimakan firaminista biyu da kuma jagoran ‘yan adawa) da kuma kara yawan ‘yan majalisa (daga 290 zuwa 360).
A cewar shugaban kasar mai barin gado Uhuru Kenyatta, wanda ya kaddamar da aikin, wannan budaddiyar madafun iko zai karkasa ka’idar “mai nasara ya dauki komai”, wanda a ganinsa shi ne sanadin tashe-tashen hankula bayan zaben Kenya.
Sai dai kudirin dokar, wanda majalisar dokokin kasar ta amince da shi a watan Mayun shekarar data gabata kuma za a kada kuri’ar raba gardama, masu sukar kudurin ne suka shigar da ita gaban kotu.
An yi zaman farko sannan kotun daukaka kara ta ce shugaban kasar ba shi da hurumin fara irin wannan aiki. Kotun ta kuma ce za a iya gurfanar da Kenyatta a gaban kotun farar hula saboda fara shari’ar ba bisa ka’ida ba.
Za a ci gaba da sauraren karar a kotun kolin har zuwa ranar Alhamis. Daga nan ne alkalan za su bayyana ranar da za su yanke hukunci.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Masu sharhi na ganin ko da kotun kolin kasar ta yanke hukunci kan gwamnati ta kuma ba da damar a shigar da dokar a zaben raba gardama, ba za a iya gudanar da zaben ba kafin zaben da aka shirya yi a ranar 9 ga watan Agusta.
Amma tun lokacin da aka kaddamar da shi a cikin shekarar 2018, BBI ta sake fasalin yanayin siyasar kasar Kenya.