Wata kotu a Morocco ta yanke wa wasu bakin haure 33 hukuncin daurin watanni 11 a gidan yari saboda samun su da shiga kasar ba bisa ka’ida ba, biyo bayan wani mummunan yunkurin tsallaka kan iyaka da jama’a suka yi a yankin Melilla na kasar Spain a watan jiya.
Akalla bakin haure 20 ne suka mutu bayan kusan mutane 2,000, da yawa daga Sudan, suka kutsa kai kan iyaka a yunkurin su na latsallakewa.
Wannan dai shi ne adadi mafi muni da aka samu a cikin shekaru da dama da yunkurin tsallakawar bakin haure zuwa yankunan Spain na Ceuta da Melilla – kasa daya tilo ta Tarayyar Turai ke da iyaka da nahiyar Afirka.
Majalisar Dinkin Duniya, Tarayyar Afirka da kungiyoyin kare hakkin bil adama sun yi tir da amfani da karfin da ya wuce kima da jami’an tsaron Morocco da na Sifaniya suka yi.
A wani labarin kuma na daban.
Legas: Mutane 2 Sun Kashe Yayin Da Wuta Ta Tashi A Wajan Sarrafa Man Fetur ‘Ba bisa Ka’ida ba
Wani wurin zubar da bola ba bisa ka’ida ba dake kusa da inda ake samar da albarkatun man fetur a cikin wani yankin da ake kanikanci na unguwar Mile 2 a Legas ya kama da wuta a ranar Talata inda mutane biyu suka mutu.
Wurin da ke tare da Barrack Signal na Sojojin Najeriya, a Mile 2, yana daukar nauyin duk wani nau’in haramtattun ayyuka.
An gano cewa direbobin tankokin mai da dama suna daukar kayayyakin daga wurin.
Kayayyakin sun hada da albarkatun man fetur da aka sarrafa ba bisa ka’ida ba, musamman rubtaccen dizal da ke wa lakabi da “Shinkafa da wake”.
An gano cewa fashewar ta afku ne daga wata tankar mai dauke da lita 33,000 na man Gas wato Automotive Gas Oil, ko kuma AGO.
Fashewar ta lashe rayukan mutane biyu tare da jikkata da dama.
Wani shaidar gani da ido ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 3.35 na yamma, yayin da ake sauke samfurin Mai din daga wata babbar mota, cikin ganguna.
Wani kuma ya kara da cewa fashewar ta faru ne sa’a daya bayan da aka hango wani jirgi mai saukar ungulu yana shawagi a kusa da garejin.
Wani Adamu Ayuba ya ce: “Mun ji karar fashewar wani abu a cikin garejin. Duk mun gudu da farko, muna tunanin harin ta’addanci ne. Amma da muka ga hayaki mai kauri da tashin wuta, sai muka sake taruwa domin kashewa amma abin ya gagara saboda wutar ta yi yawa kuma akwai wata mota da ke ɗauke da Diesel a bakin ƙofar.
Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) a shiyyar Kudu-maso-Yamma, Ibrahim Farinloye, ya ce tawagar ceto daga rundunar sojojin Nijeriya, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas (KASEMA) da Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya da ta Jiha sun kai ziyarci wurin domin kashe wutar.