By Abbas Yakubu Yaura
Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kano, a ranar Juma’a, ta yanke wa wani mutum mai suna Ado Muhammad mai shekaru 45 hukuncin daurin shekaru uku a gidan gyaran hali bisa samunsa da laifin damfarar mai kara, Nura Iliyasu, zunzurutun kudi har Naira miliyan 1.3.
Alkalin kotun, Malam Isah Rabiu-Gaya, wanda ya samu Muhammad da laifi, ya ba shi zabin biyan tarar N30,000 sannan ya kuma umurci wanda ake kara ya biya wanda ya shigar da kara kudin sa naira miliyan 1.3m.
Tun da farko, mai gabatar da kara, Mista Aliyu Abideen, ya shaida wa kotun cewa wanda ake kara ya aikata laifin ne a ranar 14 ga watan Satumbar shekarar 2021 a garin Kunya dake jihar Kano.
A cewarsa, a ranar da Iliyasu ya damka wa wanda aka yankewa hukuncin daya saya masa mota, Muhammad ya canza kudin zuwa ga amfanin kansa.
Mai gabatar da kara ya ce laifin ya ci karo da sashe na 312 da 322 na dokar Shari’ar Jihar Kano ta shekarar 2000.