Kotun ta fi da gidanka da gwamnatin jihar Kano ta kafa domin hukunta masu karya dokar hana fita cikin kwana uku kacal ta hukunta mutane fiye da 400 a jihar.
Baba Jibo,Kakakin ma’aikatar shari’a ta jihar Kano, shi ne ya tabbatarwa da manema labarai hakan a ranar Asabar a Kano.
Idan ba ku manta ba a ranar 27 ga watan Afrilu ne, shugaban kasa Buhari ya ayyana dokar hana fita a Kano har na tsawon mako biyu a wani mataki na dakile yaduwar cutar Korona.
Jibo ya ce kotun ta fi da gidanka din, an kafa su ne dama domin hukunta masu karya dokar hana fita, inda daga ranar Alhamis zuwa Asabar wadanda suka karya dokar aka sanya su yiwa al’umma hidima sakamakon karya dokar, wasu kuma aka ci su tarar naira 200 yayin da wasu kuma aka sanya su sharer yankin da aka kama su.
Har wala yau ya kara da cewa sun kama mashin din A Daidaita Sahu da mutum 11 sun karya dokar hana fita, da kuma wata mota dauke da tocila dubu daya, tana kan hanyar zuwa Falgore dake karamar hukumar Tudun Wada a jihar.
A cewarsa ababen hawan da fasinjojin da aka kama tuni aka mika zuwa ga ‘yan sanda domin bincike.
Kafin wannan dama, kotun ta hukunta mutum 135 daga ranar Litinin zuwa Talata.