Wani matashi dan shekaru 27 mai suna Maduabuchi Duru, ya shiga komar hukumar ‘yan sanda a jihar Imo yayin da yayi kokarin aikawata wata matashiya Edith Blossom fashi da makami.
Kakakin hukumar’yan sanda reshen jihar Imo dake birnin Owerri ya tabbatar da cewa lamarin ya faru a yankin Ubomiri.
Jami’in ya shaidawa manema labarai cewa “sashin binciken manyan laifuka na SARS su ne suka yi nasarar cafko sa a yayin da yake yunkurin mata fashi, kuma an kama sa da karamar bindiga kirar hannu”.
“Kuma ya amsa laifin nasa tare da wasu laifuka da ake zarginsa da aikatawa a yankin, kuma za a tura sa kotu domin yanke masa hukunci”. https://dimokuradiyya.com.ng/yan-sanda-sun-hallaka-yan-fashi-uku-a-anambra/
A wani ci gaban kuwa, shugabannin dattawan kungiyar Ijaw sun umarci shugaban hukumar’ yan sanda na jihar Legas da ya matsa bincike wajen ganin an binciko wanda yake da hannu wajen mutuwar Steven Doubra Legbe wanda aka kashe a rukunin gidaje na Victoria.
Rahotanni sun gabata cewa, kafin mutuwar Legbe ya samu dan sabanin da wani dilallin gidaje.
Hukumar ‘yan sanda tayi kokarin kwantar da tarzomar da take shirin tashi a dalilin kisan da aka yiwa mamacin, wanda wasu fusatattun matasa suka ce lallai sai sun binciko tare da hukunta wanda ya aikata wannan mummuna laifi.
A cikin wani jawabi da shugaban dattawan kungiyar ta Ijaw yace ya kamata hukuma tayi aikinta don ganin an zakulo wanda ya kashe Steven Doubra Legbe.