‘Koyi Da Manzon Allah (S.A.W) Ya Sa Na Auri Matar Da Ta Girme Ni Da Shekaru 11’
Jarman Bakori, Santurakin Galadiman Katsina,Alhaji Halliru Sa’ad Malami
A wannan makon ne tawagar ’yan jarida ta tattauna da Jarman Bakori, San Turakin Galadiman Katsina, Alhaji Halliru Sa’ad Malami a kan kiriro guraban aikin yi ga jama’ar garin Malumfashi fiye da 300 ta hanyar kafa katafaren kamfanin sarrafa shinkafa, man gyada da kuma wajen yin gadaje da kujeri irin na zamani da takalma domin taimaka wa al’umma wajen rage masu zaman kashe wando da kuma samar masu da hanyoyin dogoro da kai.
Kodayake a cikin hirar ya bayyana muhimmancin jama’a su rika yi wa ’yan siyasar da suka zaba suka tura su wakilce su a matakai daban-daban hisabi don gano kamun ludayinsu, ya ce bai da alaka da siyasa, sai dai yana tare da su ’yan siyasa, amma bai da sha’awar tsayawa wani mukamin siyasa. Ya bukaci mutane su cire kwadayi, zarmiyya, fadanci da raina na gaba in har suna son hakar su ta cimma ruwa a rayuwa.
Kwararre a harkar gine-gine, fasahar kasuwanci da kuma kayan kawa, wanda aka haifa a shekara 1982, wanda ya yi karatunsa a Malumfashi, Funtuwa, Abuja, Amurka da Dubai, ya yi wa manema labarai karin haske a kan yadda aurensa da tsohuwar matar Gwamnan Jihar Taraba; Danbaba Suntai ya kasance da kuma dalilin da ya sa ya ja bakinsa ya yi shiru tun wancan lokacin sai yanzu ya bara.
TAMBAYA: Watanni biyar da suka gabata an yi ta magana a kan yadda ka auri matar tsohon Gwamnan Jihar Taraba, Marigayi Danbaba Suntai, Hajiya Hawwa, me ya ba ka karfin gwiwar aurenta?
ALHAJI HALLIRU SA’AD MALAMI: Na yi ta kokarin kauce wa ’yan jarida a wancan lokacin. A matsayina na Musulmi na yi imani da kaddara. Na yi koyi da Manzon Allah (S) a kan yadda ya auri Nana Khadija. Hawwa shekarunta 47, ni kuma 36 a tsakanin mu shekaru 11. Ba wata tazara ce a tsakaninmu ba. Idan muka ce muna aikata wani abu na addini, na yin wani abu da za ka yi wanda za a yi koyi da kai na addini ko na gaskiya, ba za ka yi shi da baki ba, za ka yi shi ne a aikace. Ka ga shi kuma Maulumfashi, wannan shi ne garin da nake. Za ka iya ganin komai da kanku. Mutane sun fadi maganganu kala-kala, wasu sun ce ma ni Kwamishina ne a Jihar Taraba. Ni dai ban taba aiki da Danbaba Suntai ba. Duk wadannan ba gaskiya ba ne. Ban taba rike wani mukamin siyasa ba a Taraba. Na ga Danbaba Suntai ne sau biyu a rayuwarta, a lokacin da yake Gwamna in ya zo gidan Malam Umaru Musa ’Yar’aduwa. Ba mu dade da shakuwa da Hawwa ba, sai maganar aure ta shiga tsakanin mu. Daga nan sai muka shaku tamkar ’yan’uwan juna. Ban yi shirin aure a tsakanin mu ba, amma sai Allah ya kaddara. A wancan lokacin na tsara cewa ba zan shiga cece-kuce a tsakani na da mutane ba. Na yanke shawarar ba zan yi magana ba, balle mai da martani ga surutan mutane. Abin da ya fi dacewa shi ne ka kame, ka yi hakuri. Sai ka yi magana a daidai lolacin da ya dace. Ina son in fada maka, an fadi abubuwa da yawa a kanmu, ni da Hawwa. Ina so ka sani ni dan kasuwa ne da mutane sama da 1700 ke cin abinci a karkashina. Na tabbatar ba kowane Gwamna ne ya samar wa mutane masu yawa haka hanyar cin abinci ba.
Na yanke shawarar auren Hawwa ne saboda na ba da misali, na zama wanda mutane za su yi koyi da ni. Bari in ba ka misali, a bambancin shekaru 11 da ke tsakanin mu da Hawwa, a lokacin da take shekara 21, ni kuma ina da shekara 10, a wannan lokacin babu yadda za a yi ta yi tunanin za ta auri mutum kamar ni. Sai dai Allah yana da hanyoyin da yake tabbatar da wasu abubuwan da ya bar wa kansa sani. Kalli abokaina da muka taso tare, mun yi makaranta tare. Allah ya nufi ya fito da ni daga cikin su ba don ina da wani abu da ya fi su ba, na yi imani da Allah, a lokaci guda shi yake tsara abubuwan da za su faru.
TAMBAYA: A baya ka ce, kana da burin samar wa mutane aikin yi, ta wace hanya auren da kuka yi da Hajiya Hawwa zai taimaka wajen tabbatar da wannan burin naka?
AMSA: Al’amarin aure ko na rayuwa, duk abin da ka ce ka bar wa Allah ya yi maka, ko mai daren dadewa zai tabbata. Hawwa tana da kyakkyawar manufa wajen tabbatar da wannan burin nawa. Ka ga dai a lokacin da Gwamnan Taraba bai da lafiya na tsawon shekaru uku ita ce tamkar Gwamna a wannan lokacin, don haka tunda ka ga Allah ya kaddara ya hada mu da Hawwa, lallai zai yi amfani da ita ne wajen gabatarwa ko aiwatar da wani abu da ya dace.
TAMBAYA: Kamar ka karya wani kwari na auren wata matar wani babba da aka saba in sun rasu akan rasa mai aurensu?
AMSA: Kamar yadda na fada maka ita rayuwa ba ka taba sanin abun da zai zo maka a gaba ba. Da Gwamna da matarsa, da Shugaban kasa da matarsa duk mutane ne ’yan’adam daidai da kowa, abin da kawai za ka lura da shi, shi ne in har za ka bai wa wani mutum tazarar shekara 11, kuma ka amince ka aure shi, akwai wani abu kyakkyawa da ka gani a tare da shi. Na yi imani cewa idan Allah zai fitar da ni daga nan a cikin kuruciyata ya kai ni wani wajen in rayu ba tare da Uwa ko Uba ba, ko kuma wani dan’uwana na jini ba, Allah zai taimake ni wajen tabbatar da manufata. Kuma zai kare ni ba wani abu da zai faru da ni insha Allah.
TAMBAYA: Ka bude kamfanin sarrafa shinkafa da wajen gurza man gyada da auduga a wannan garin naku, me ya sa ka zabi yin hakan a Malumfashi?
AMSA: Kamar yadda na fada a baya, Malumfashi na cikin Kananan Hukumomin da ke Nijeriya da ba za ka kirga Kananan Hukumomi biyar ba a kasar nan ba tare da ka ambace ta ba. Mutanen wannan garin suna bi na bashi. Ina ji a jikina akawai nauyin da ya rataya a wuyana wajen inganta rayuwar jama’ar wannan yankin. Idan ka bincika jama’a za su fada maka a 2008 na sayi manyan motocin daukar kaya 33 na bayar don samar wa jama’a aikin yi. A shekarun baya wannan garin namu yana hadar-hadar kasuwanci. A da in ka fito a garin nan za ka manyan motoci DAF sama da 100 sun yi lodi zuwa Kudu. A lokacin na yi tunanin wace gudummawa zan bai wa jama’a don su amfana. Shi ya sa na sayo manyan motoci 33 don mu gwada. A wancan lokacin na samar wa mutane fiye da 400 aiki. Amma irin yadda suka wulakanta da kashe motocin a lokacin kankani ban ji dadi ba.
A wannan lokacin Malam Umar Musa ’Yar’aduwa yana Shugaban kasa aka yi haka. A lokacin na yanke shawara in zauna a Malumfashi, in ka tambayi jama’a za su fada maka ina kwanaki hudu a Malumfashi, sauran kwanakin kuma in yi su a Abuja. A wancan lokacin in dai ba ka gan ni a Malumfashi ba, to ban kasar. Ban da wajen da zan je in rayu in ji dadi sama da Malumfashi.
Tun da na zo garin nan daurin aure da nufin in kwana daya in koma, amma sai hakan ta gagara, saboda yadda na ga mutane suna bukatar gudummawar da za ta inganta rayuwarsu. An ce min an ga macizai a cikin gidan nan da kuma ma’aikatar da nake ginawa, sai na sa aka nemo mutane na ba su aikin cire ciyayin da ke wajen da aka ga macizan. Kofar gidana a bude take, na ga ba wanda ya biyo ni yana neman in ba shi wani abu, sabanin yadda suke yi a baya. Wannan abin ya canza min tunanina. Na ce bai kamata in hukunta mutane da laifin da wasu suka yi ba. Sai na yanke shawarar farfado da wannan masana’atar da na fara ginawa tun shekaru hudu da suka wuce.
Katafaren kamfanin sarrafa shinkafa ne na zamani, Turawa muka gayyato za su kakkafa injinin da za mu yi aiki da su a wannan kamfanin. Akwai wajen sarrafa man gyada da auduga da kuma wajen yin gadaje da kujeri irin na zamani, irin wadanda ake sayowa a Turai. A lokaci guda da kamfanin yin takalma a wajen saboda ina son in kirkiro wa mutane 300 aiki a rana daya.
Abu na farko na fahimci mafi yawan mutanen da ka ga suna zaune, ko suke shaye-shaye, ko sata, ko kuma wani ya yi amfani da su wajen cimma burinsa na siyasa, don ba su samu abin yi ba ne. Abu na biyu jarabawa ce na samu da rashi, in ba a samu mai karfin imani ba, zai yi amfani da wannan rashin ya yi abin da ransa ya ga dama. Haka samu, idan Allah ya daga ka a tsakanin mutane, in ba a samu mai karfin imani ba, zai dauka shi ya fi kowa kwakwalwa, tunani da ilimi, alhali kuwa yana yaudarar kansa ne, saboda wani abu na shirme. Ga abokan karatuna nan, da yawansu sun fi ni kokari a lokacin da muke makaranta, amma yau ba Maulufashi, ko Abuja ba, a Nijeriya gaba daya in ka kira sunan, nan da nan za a ce maka an san ni. Ka ga wannan ba yin kaina ba ne, Allah ne. Wannan matsayin da nake a kai shi ne muhimmi, don haka wane abu zan yi wajen taimakon al’ummata. Ba zai yiwu ba muna matasa, yawanmu ya kai wajen 70% a cikin al’ummar nan, amma a ce muna rayuwa ba tare da abin yi ba. Idan ka duba kudancin kasar nan, misali a Lagos, Ibadan da Fatakwal, za ka ga fiye da kashi 95% na mutane ba su dogara da gwamnati ba, mafi yawansu ba ofis suke zuwa ba, suna yin sana’a ne. Ka ga dai sun fi mu ilimi, amma Allah ya yi amfani da mu Arewa mu zama uwa-uba a kasar nan, amma saboda son zuciya na wasu daga cikin shugabanninmu an kashe zuciyar matasanmu. Kowa zuciyarsa ta mutu. In ka je ka hadu da mutum wanda bai taba rike Naira dubu 100 ba, balle ya rike Naira miliyan daya, za ka gan shi yana yawo da takardun fili, yana maganar zai sai dai gidan miliyan 100, don ya samu kaso mai tsoka da zai sa ya zama mai kudin dare daya. Za ka samu mutanenmu idan suka ga Gwamna ko Sanata zai zo, suna rawar jiki, amma ba zai saurare su ba. Alhali mutane ba su sani ba, daga Shugaban kasa zuwa Gwamna, wadannan mutanen da suke dauka ba a bakin komai ba, sune suka samar masu abin yi, domin in ba don wannan mukamin da suka zabe su suka dora su a kai ba, su ba kowa ba ne.
Daga baya sai na fahimci lallai ya kamata mu tashi mu yi wa kanmu fada, mu cire kwadayi, mu rayu cikin imani, komai za mu yi, mu yi shi don Allah. Domin duk lokacin da ka je ka zabi wani saboda dan kudin da zai ba ka da ba su taka kara suka karya ba, za ka sai da ’yancinka ne na tsawon shekaru hudu. Idan siyasa ta zo yau ka zabi dan siyasa, wani sai ya shekara bai sake leke wa mazabarsa ba. Wani ma sai ana sauran wata shida zabe zai zo yana raba wa mutane kudade da kayan bukatu. Idan ya raina hankalin mutane sai ya ajiye masu SA a garuruwansu wadanda za su rika amsar koke-kokensu, duk maganar da za ka yi da Honarabul sai dai ku yi ta da SA, sai a dan turo maku dan wani abu.
Bari in fada maku wani abu, ya kamata ya zamato mu na kasa mun san darajar babba, kada ka kunyata ko ka zagi Shugabanka, amma damarka ce ka samar masa abin yi. Abin da ya sa na yanke shawarar yin wannan maganar, saboda yanzu take da amfani, ba wanda zai kalle ni ya ce ina wannan maganar ne saboda zabe ya kusa ina son zama wani abu. In ka tambayi duk wanda yake a nan garin, ban tsoma kaina a cikin duk wani abu na siyasa ba. Amma bari in fada maku cewa ya kamata a samu mutane su kafa kungiya ba da rashin kunya ba, da biyayya da girmamawa, su nemi ganin Gwamna ya ba su lokaci ko a Kafur ko a Katsina, su tambaye shi sun sake zaben sa da alkawarin zai yi masu kaza da kaza, su ce masa suna son sanin mene ne tsarinka ga matasa da iyaye da kakanninmu? Sai wani ya daga hannu ya mike ya ce mai girma Gwamna ya al’amarin tsaro, me ake ciki a kan wannan matsalar tsaro da ta taddabe mu? Mene ne shirinka na yadda za a warware wannan matsalar da ke ci mana tuwo a kwarya? Sai a ba shi shawara. Idan Gwamna ya yi maku bayani sai ku dawo ku fada wa mutanen Malumfashi ga alkawarin da Gwamna ya yi mana. In ba a ciki alkawarin ba, sai ku sake komawa ku tunatar da shi. A haka za a ci gaba har zuwa lokacin da hakarku za ta cimma ruwa. Ka ga wannan zai nuna wa Gwamna, ko kuma wani zababbe cewa mutanen da yake wakilta kansu ya fara wayewa.