Majalisar Wakilai ta Ƙasa, ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta maida kuɗaɗen da Ibori ya sata, Fam Miliyan 4.2 ga Jihar Delta.
Wannan ya biyo bayan ƙudirin da ‘yan majalisar daga jihar Delta suka gabatar wa majalisar ne a Larabar da ta gabata.
Haka nan, ‘yan majalisar sun ce jimillar kuɗin Fam miliyan 6.2 ne amma ba milyan 4.2 ba kamar yadda aka ruwaito.
Bugu da ƙari, Majalisar ta buƙaci Ma’aikatar Kuɗi ta Kasa da ta bai wa Babban Lauyan Gwamnati kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, umarnin ya miƙa wa Majalisar dukkan takardun da ke da alaƙa da batun kuɗaɗen.
Shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilan ƙasar ne ya gabatar da ƙudurin yana cewa kamata ya yi a saka kuɗin a cikin asusun gwamnatin jihar Delta, ba asusun gwamnatin Tarayya ba.
Majalisar wakilan ta amince a turo da kwamatoci zuwa wurin ministar kuɗi da ministan shari’a domin su tattauna da juna a kan ko wani ɓangare ya kamata a bai wa kuɗin.
Sai dai tun farko ministan sharia na Najeriya Abubakar Malami ya ce ba bu wani shiri da ya wajabta maida kuɗin ga gwamnatin jihar Delta.
Amma Hon Abdurrazak Namdas wanda mamba ne a majalisar wakilan ya ce yana da muhimmanci a warware wannan rigimar .
Tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori ne ya sace kuɗin kuma ya kai ƙasar Burtaniya, inda aka kama shi da laifi.